EFCC Ta Tona Yadda Wasu Sarakuna Ke Haɗa Baki da Masu Laifi a Najeriya
- Shugaban EFCC na ƙasa, Mr Ola Olukoyede ya yi ikirarin cewa sarakuna na da hannu a ayyukan haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba
- Ya ce haramtaccen aikin haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida yana ɗaya daga cikin abubuwan da ke kawo gurɓatar muhalli a wasu sassa
- Mista Oluƙoyede ya faɗi hakane a wurin taron da aka shirya kan cin hanci da rashawa da kuma sauyin yanayi ranar Talata a Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arziki zagon ƙasa (EFCC) ta ce sarakuna na da hannu a aikin haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba a ƙasar nan.
Hukumar EFCC ta ce duk da sarakuna sun san illar haƙar ma'aidanai ta haramtacciyar hanya, amma suna ba masu haƙar haɗin kai saboda za a ba su ɗan na goro.
Shugaban EFCC na ƙasa, Mr Ola Olukoyede ne ya bayyana hakan a wani taro da ƙungiyar HEDA ta shirya kan cin hanci da sauyin yanayi a Abuja ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daily Trust ta tattaro cewa cibiyar 'HEDA Resource Centre' tare da haɗin guiwar Hawkmoth da gidauniyar MacArthur ne suka shirya taron a Abuja.
EFCC ta faɗi illar satar ma'adanai
A rahoton Punch, shugaban EFCC na ƙasa ya ce:
"Idan muna magana kan abubuwan da ke gurɓata muhalli, dole mu ambaci haƙar ma'adabai ba bisa ƙa'ida, a shekaru biyar masu zuwa abin zai ƙara muni fiye da iillar haƙo ɗanyen mai."
"Don haka mu sa a ran mu, wannan ne babbar matsalar, da za ku ga hotunan yadda haƙar ma'adanai ya lalata muhallai za ku sha mamaki, kuma ba ƴan kasar waje ke yi ba, mutanen mu ne."
"Mutanenmu ne suke yin abin da zai illata muhallan da suke rayuwa a ciki, a wasu lokutan sarakuna ne ke ɗaure masu gindi."
Olukoyede ya ɗora laifin gurɓatar muhalli a Neja Delta kama daga malalar mai da sauransu kan cin hanci da rashawa.
Hukumar EFCC ta kamo Yahaya Bello
A wani rahoton kuma hukumar yaki rashawa ta EFCC ta ce za a gurfanar da Yahaya Bello, tsohon gwamnan jihar Kogi a gaban kuliya
Hukumar ta tuhumi Yahaya Bello ne da laifin karkatar da kudi, zagon kasa da kuma sama da fadi da kimanin da N80bn lokacin yana ofis.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng