Karin Kudin Fetur: NLC Ta Fusata, Ta Bayyana Muguwar Yaudarar da Tinubu Ya Yi Mata
- Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta yi martani mai zafi kan ƙarin kuɗin man fetur da aka yi a ƙasar nan a farkon makon nan
- NLC ta bayyana cewa shugaba Bola Tinubu ya yaudare ta tare da sauran ƴan Najeriya sakamakon ƙarin kuɗin fetur da aka yi
- Ta bayyana cewa ba haka suka yi da Tinubu ba lokacin da suke tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yaudare su.
Ƙungiyar ƙwadagon ta bayyana cewa shugaba Bola Tinubu ya yaudari ƴan ƙwadago da sauran ƴan Najeriya sakamakon ƙarin kuɗin man fetur da ƙarancinsa da ake fama da shi a ƙasar nan.
Martanin NLC kan ƙarin kuɗin fetur
Shugaban NLC na ƙasa, Joe Ajaero ne ya bayyana hakan ranar Talata a cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta sanya a shafinta na yanar gizo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƙungiyar ta yi martani ne kan ƙarin kuɗin man fetur da aka yi wanda ta bayyana a matsayin abin tashin hankali.
Yadda Bola Tinubu ya yaudari NLC
Joe Ajaero ya bayyana cewa Tinubu ya fadawa NLC da TUC yayin tattaunawa kan mafi ƙarancin albashi cewa su zaɓi tsakanin N250,000 da ƙarin kuɗin fetur ko su yarda da N70,000 a bar farashin fetur yadda yake.
"Mun tuna lokacin da shugaban ƙasa ya ba mu zaɓin ko dai N250,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi tare da ƙara farashin fetur zuwa N1,500 ko N2,000, da N70,000 a bar farashin fetur ya tsaya yadda yake."
"Mun zaɓi a biya N70,000 saboda ba mu son mu ƙara jefa ƴan Najeriya cikin wahala."
"Amma sai ga shi ƙasa da wata ɗaya gwamnati ta kasa fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin kuma ta ƙara kuɗin man fetur. Wannan babban tashin hankali ne."
"Amma idan za a faɗi gaskiya, wannan yaudarar ta yi daidai da halin wannan gwamnatin domin ta saba yin hakan."
- Joe Ajaero
Gwamnatin Tinubu ta musanta ƙara kuɗin fetur
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta musanta cewa ita ce ta umarci kamfanin mai na kasa (NNPCL) da ya kara kudin man fetur zuwa N1000 zuwa sama.
Gwamnatin ta ce rahoton da ke yawo na cewa ministan albarkatun fetur, Heineken Lokpobiri ne ya umarci kara farashin fetur ba gaskiya ba ne.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng