'Yan Sandan Kano da Kaduna Sun Hada Kai, An Ceto Budurwa da Ta Kwana 35 Hannun Miyagu

'Yan Sandan Kano da Kaduna Sun Hada Kai, An Ceto Budurwa da Ta Kwana 35 Hannun Miyagu

  • Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta yi holin wasu mutane biyu bisa zargin sace wata matashiya 'yar shekara 20 da haihuwa
  • An sace Hafsa ne daga garin Zarewa, karamar hukumar Rogo a jihar Kano bayan mahaifinta ya shigar da korafi rundunar yan sanda
  • Jam'in hulda da jama'a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa an yi nasarar ceto budurwar ba ko sisi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta yi holin wasu masu garkuwa da mutane guda biyu da aka yi nasarar cafkewa a Kaduna.

Mutanen biyu sun sace Hafsa, budurwa mai shekara 20 daga gidansu da ke Zarewa bayan an lakadawa mahaifin yarinyar, Alhaji Nuhu Zarewa dukan kawo wuka.

Kara karanta wannan

Bayan karbe kudin fansa N17m, miyagu sun saba alkawari, sun kashe 'dan shekara 19

Kidnappers
An kama miyagu biyu tare da ceto wadanda su ka sace Hoto: Abdullahi Kiyawa
Asali: Facebook

A bidiyon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, kakakin rundunar 'yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa miyagun sun nemi kudin fansa N30m.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Miyagu sun shiga hannun yan sanda

Rundunar 'yan sandan Kano ta kubutar da Hafsa da miyagu su ka sace zuwa Kaduna, inda likitoci su ka tabbatar da cewa ba a taba mutuncinta ba.

Haka kuma an yi nasarar ceto wani dattijo wanda miyagun su ka hada da budurwar a dajin da ke Makarfi da ke jihar Kaduna, sannan an damke mutanen da ake zargi.

Matashiya ta kubuta daga wajen miyagu

Mahaifin Hafsa, Nuhu Zarewa ya ce akalla miyagu 10 ne su ka shiga gidansa inda su ka yi masa dukan tsiya, tare da dauke 'yarsa.

Alhaji Zarewa ya bayyana cewa bai biya ko sisi ba kafin rundunar 'yan sanda ta kubutar da 'yarsa ba, inda ya yi ta godiya da addu'ar alheri ga 'yan sanda.

Kara karanta wannan

Sojoji sun cafke masu kai wa 'yan ta'adda miyagun kwayoyi a Arewa maso Gabas

Daga cikin miyagun da aka kama akwai Yakubu Abubakar mai shekaru 40, wanda aikinsa shi ne tsaron mutanen da aka sato a kan N50,000.

An hallaka miyagu a Kaduna

A wani labarin kun ji cewa rundunar sojojin kasar nan ta yi namijin aikin hallaka miyagu akalla guda takwas da su ka addabi mazauna karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.

Gwamnatin Kaduna ta bakin kwamshinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ne ta tabbatar da nasarar, inda ya kara da cewa jami'an da ke sintiri ne su ka yi gagarumin aikin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.