Farashin Man Fetur Ya Ƙara Tashi, Kowace Lita Ta Haura N1,000 a Kano
- Ƙarancin man fetur ya ƙara tsananta yayin da farashin lita ya kai N1,200 a gidajen man ƴan kasuwa a jihar Kano ranar Talata
- Rahotanni sun nuna cewa farashin ya tashi zuwa N904 a gidajen man kamfanin NNPCL, masu ababen hawa sun yi layi suna jira
- Wani ma'aikaci a ɗaya daga cikin gidan man NNPC ya ce sun wayi gari ne da ƙarin amma har yanzu suna jiran a ba su umarni
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Farashin litar man fetur ya tashi zuwa N1,200 a mafi yawan gidajen mai a birnin Kano yayin da gidajen man NNPC ke sayarda lita kan N904.
Rahotanni sun nuna ƙarancin man ya kara tsananta a sassan ƙasar nan, masu ababen hawa sun yi dogon layi a gidajen mai musamman na NNPC.
Yadda NNPC ya ƙara farashin man fetur
Wani ma'aikaci a ɗaya daga cikin gidajen man NNPC ya shaidawa Daily Trust cewa suna jiran umarni ne daga sama gabanin fara sayar da fetur a sabon farashi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ma'aikacin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce:
"Mun fito aiki yau (Talata) da safe muka kunna inji ba zato muka ga an yi ƙari, yanzu haka dai muna jiran umarni kafin mu fara sayarwa," in ji shi.
Ƴan Najeriya sun koka da ƙarin kuɗin fetur
Wani mai mota, Isah Muhammad wanda ke cikin dogon layin ababen hawa ya nuna damuwarsa kan ƙarin farashin da aka yi.
"Ina muka dosa a kasar nan? Ina ake son talaka ya sa ransa? Abin da ban haushi, muna gani ake mana haka," in ji shi.
Har ila yau wani direban mota duk dai a Kano, Ibrahim Saleh ya tuna lokacin da yake sana'ar bunburutu a lokacin mulkin marigayi Ƴar'adua.
"Ina tuna lokacin da nake sana'ar sayar da mai, lokacin ana sayar da lita N95. Wata rana mun je sayen mai a lokacin mulkin Ƴar'adua, kawai aka hana ba da mai.
"Duk mun saduda za a ƙara kuɗin mai amma kawai suka rage shi zuwa N65, ba na manta wannan, har yanzun ina tuna abin a rayuwata."
Legit Hausa ta tuntuɓi wani mazaunin Hotoro a jihar Kano, Sanusi Isiyaku, wanda ya tabbatar mana da halin da ake ciki musamman dogon layin ababen hawa a gidan mai.
Sanusi ya ce mutane na cikin wahala da tsadar rayuwa, wannan ƙarin da aka yi zai ƙara jefa talakawa cikin ƙaƙanikayi.
Ya ce:
"Na yi mamakin layin da na gani a gidan man NNPC da safe, duk da ana samun layi idan akwai mai amma na yau ya fi muni, ina ake son mu sa kanmu ne.
"Sun cire tallafi mun haƙura to a samar mana da man mana, da kuɗinmu fa zamu siya. Mun wayi gari da labari mai daɗi na fara aikin matatar Ɗangote, taya tsada za ta biyo baya?"
Matatar Ɗangote ta gabatar da sumfurin mai
Kuna da labarin matatar man Ɗangote ta gabatar da sumfurin farko na man fetur ɗin da ta tace wanda zai shiga kasuwa nan gaba kaɗan.
Alhaji Aliko Ɗangote shi ne ya bayyana sumfurin yayin zantawa da ƴan jarida ranar Talata da safe a matatar da ke a jihar Legas.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng