'Yan Ta'adda za Su Shiga Uku, Ministan Tsaro da Hafsoshin Sojoji Sun Isa Sakkwato

'Yan Ta'adda za Su Shiga Uku, Ministan Tsaro da Hafsoshin Sojoji Sun Isa Sakkwato

  • Jagororin tsaron kasar nan sun amsa umarnin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yunkura domin kakkabe rashin tsaro a Sakkwato
  • Shugaban kasar ya kuma ba su umarnin su tattara kayansu su koma jihar ta Sakkwato da zama har sai an shawo kan matsalar tsaro a yankin
  • A yau ne karamin Ministan tsaro, Dr. Bello Matawalle da sauran jagororin hukumomin tsaro su ka sauka a jihar Sakkwato domin fara aiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Sokoto - Karamin Ministan tsaro, Dr. Bello Matawalle ya shiga gaba inda ya jagoranci hafsoshin tsaron kasar nan zuwa babban jihar Sakkwato kan rashin tsaro.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun shiga uku: Gwamnati ta ba hafsoshin tsaro umarnin tarewa a Sokoto

A baya, gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta umarci hafsoshin tsaron su tare a jihar Sakkwato domin fatattakar miyagun da su ka hana mazauna garin sakewa.

Sokoto
Jagororin tsaro sun sauka a jihar Sakkwato Hoto: @Barde6767
Asali: Twitter

A sakon da Bashir Ahmad, hadimin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya wallafa a shafinsa na X, ya nuna cewa shugabannin tsaron sun sauka a jihar Sakkwato a yau Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa zuwa jihar Sakkwaton ya biyo bayan shirin da ake yi na dakile 'yan ta'adda da ke jihar domin magance matsalar tsaro.

Hafsoshin tsaro sun sauka a Sakkwato

Channels Television ta wallafa cewa hafsan hafsoshin kasar, Janar Christopher Musa da sauran jagororin tsaro sun sauka a jihar Sakkwato.

An hango Janar Christopher Musa da wasu shugabannin tsaro tare da karamin Ministan tsaro kuma tsohon gwamnan Zamfara, Bello Matawalle a Sakkwato.

Matakin wani shiri ne na tsaurara tsaro da tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a jihohin Arewa ciki har da Zamfara, Kebbi, Sakkwato, Katsina da sauran jihohi a yankin.

Kara karanta wannan

Ma’aikatun gwamnatin tarayya 3 da ba su da Ministoci a mulkin Bola Tinubu

An ba jami'an tsaro umarnin komawa Sakkwato

A baya mun ruwaito cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya umarci hafsoshin tsaron kasar nan su tattara kayansu su koma jihar Sakkwato domin dakile matsalar tsaro da ta addabi yankin.

Haka kuma matakin zai kawo sauki a kan yadda yan ta'adda ke cin karensu babu babbaka a jihohin Arewa maso Yamma, inda yanzu kullum ake samun rahoton garkuwa ko kashe jama'a.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.