Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawa da Shugaban China, an Samu Bayanai
- Bola Ahmed Tinubu ya shiga ganawa da takwaransa na ƙasar China, Xi Jinping a ranar Talata, 3 ga watan Satumban 2024
- Shugabannin ƙasashen biyu na jagorantar wani taro ne wanda ake sa ran zai kai ga cimma yarjeniyoyin bunƙasa tattalin arziƙi
- Ganawar shugabannin ƙasashen biyu na zuwa ne yayin da Tinubu ke ci gaba da ziyarar aiki da ya kai a ƙasar da ke yankin Asia
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Kasar China - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya shiga ganawa da shugaban ƙasar China, Xi Jinping.
Shugabannin ƙasashen biyu na jagorantar wani taro ne wanda ake sa ran zai kai ga rattaɓa hannu kan yarjejeniyoyin bunƙasa tattalin arziƙi da ƙarfafa dangantakar da ke tsakaninsu.
Hadimin Bola Tinubu kan kafafen sadarwa na zamani, Dada Olusegun ya sanya bidiyon tattaunawar da ake yi a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Menene manufar taron Najeriya da China?
Ana sa ran taron da ake yi ci gaba da yi zai sa a rattaɓa hannu kan yarjejeniyoyin fahimtar juna a ɓangarori daban-daban waɗanda za su zurfafa haɗin gwiwa a tsakanin ƙasashen biyu.
Ɓangarorin da ake sa ran za su rattaɓa hannu kan yarjeniyoyin sun haɗa da fannin tattalin arziƙi, fannin noma, bunƙasa fasahar tauraron ɗan adam, bunƙasa tattalin arziƙin teku, da dai sauransu.
A makon da ya gabata ne mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ya shaidawa manema labarai a fadar gwamnati da ke Abuja, cewa ɗaya daga cikin dalilan ziyarar aikin, shi ne tattaunawa a tsakanin shugabannin ƙasashen biyu.
Karanta wasu labaran kan Tinubu
- Shugaba Bola Tinubu ya isa kasar China, bidiyo ya bayyana
- Tura ta kai bango: Ana hasashen Tinubu zai sallami wasu Ministocinsa, za a yi gyara
- Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan 'umarnin' kara farashin litar man fetur
Shekarau ya yabawa Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau ya yi magana kan naɗe-naɗen shugabannin tsaro da Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi.
Shekarau ya yabawa Shugaba Bola Tinubu kan naɗin shugabannin tsaro daga yankin Kudu maso Yammacin ƙasar nan, inda ya yi fatan su yi abin da ya dace.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng