"Shugaba Tinubu ne Zai Kayyade Farashi," Dangote Ya Fadi Lokacin Fadan Kudin Litar Fetur

"Shugaba Tinubu ne Zai Kayyade Farashi," Dangote Ya Fadi Lokacin Fadan Kudin Litar Fetur

  • Hamshakin dan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa ya na jiran majalisar zartarwa ta kasa da shugaba Bola Tinubu kan farashin fetur
  • Alhaji Dangote ya bayyana haka ne yayin da 'yan Najeriya ke jiran lokacin da matatarsa za ta fara fitar da tataccen fetur daga matatarsa ga yan kasa
  • Ya bayyana cewa ko a yau shugaba Tinubu ya kammala amincewa da farashin litar man fetur, a yau matatarsa za ta fitar da fetur zuwa gidajen mai

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Legas - Hamshakin dan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa majalisar zartarwar kasar nan karkashin jagorancin shugaba Bola Tinubu ce za su tsayar da farashin litar mai daga matatarsa.

Kara karanta wannan

Ana murna matatar Dangote ta fara samar da fetur, NNPCL ya kara farashin litar mai

Alhaji Dangote ya bayyana haka ne a yau Talata jim kadan bayan ya nunawa yan Najeriya samfurin man fetur din da matatarsa ta fara tacewa.

Ekiti Princess Gloria
Kamfanin Dangote ya ce shugaba Tinubu ne zai fadi farashin fetur din matatarsa Hoto: Ekiti Princess Gloria
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Alhaji Dangote ya ce nan da awanni 48 kamfaninsa zai fara fitar da tatacce kuma ingantaccen fetur zuwa gidan mai idan an tsayar da farashin farashi lita.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dangote ya yaba da sayar masa danyen mai

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana jin dadin yadda gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta amince a fara sayar masa danyen mai a farashin Naira.

A watan Yuni ne shugaban kasa, Tinubu ya amince da fara sayarwa matatar Dangote danyen fetur a Naira domin saukaka farashin man da za a tace a kasar, Daily Post ta wallafa.

Feturin Dangote zai kawo sauki?

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 7 da Dangote ya fada yayin fara fitar da man fetur a matatarsa

Matatar man Dangote ta bayyana cewa fetur din da matatarsa za ta samar zai saukaka karancin mai da dogayen layi da ake fama da shi.

Kan sayarwa matatar fetur da Naira, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa matakin zai rage bukatar canjin kudin kasashen waje da 40%.

Matatar Dangote ta gabatar da fetur

A wani labarin kun ji cewa matatar man Dangote ta fitar da samfurin tataccen fetur da aka samar a matatar da zimmar fara sayarwa 'yan Najeriya da zarar shugaba Bola Tinubu ya amince.

Shugaban rukunin kamfanin Dangote, Aliko Dangote ya bayyana godiya ga 'yan Najeriya da shugaba Bola Tinubu bisa goyon baya da suka ba shi har aka samun nasara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.