Ana Murna Matatar Dangote Ta Fara Samar da Fetur, NNPCL Ya Kara Farashin Litar Mai
- Ana murna matatar Aliko Dangote ta fara samar da man fetur, kamfanin man NNPCL ya kara farashin mai a gidajensa
- Wasu gidajen sun kara kudin litar mai daga N568 zuwa N855 har N897 a wasu wuraren da rahotanni suka tabbatar a yau
- Wannan na zuwa ne yayin da ake cikin mawuyacin hali na tsadar rayuwa tun bayan cire tallafin mai a kasar baki daya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku
FCT, Abuja - Kamfanin mai na NNPCL ya kara farashin litar mai a mafi yawan wurare a fadin Najeriya.
A mafi yawan gidajen mai musamman na kamfanin NNPCL, an kara kuɗin har zuwa N855 kan farashin lita da a baya ake siyarwa N568.
NNPCL ya sake daga farashin litar mai
Daily Trust ta tabbatar da cewa an kara farashin litar ne yayin da matatar Dangote ke shirin fara samar da fetur a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu gidajen mai na musamman na NNPCL suna siyar da litar har N897 daga N568 a baya.
Hakan na zuwa ne kwana biyu bayan matatar Dangote ta tabbatar da fara fitar da man fetur a kasar domin saukakawa al'umma.
Wane martani NNPCL ya yi kan farashin?
Sai dai zuwa yanzu kamfanin bai fitar da sanarwar a hukumance kan karin farashin ba kamar yadda ake yadawa, cewar rahoton Vanguard.
Karin farashin na zuwa ne awanni 48 bayan kamfanin ya yi korafin yana bin masu shigo da mai kasar bashin N6bn.
Hakan ya biyo bayan karyata zancen a lokuta da dama a baya kafin tabbatar da hakan a ranar Lahadi 1 ga watan Satumbar 2024.
Tattaunawar Legit Hausa da mai saida mai
Wakilin Legit Hausa ya zagaya gidajen mai da dama a Gombe inda ya tarar a kulle.
Sai dai ya samu tabbacin cewa an fara ba da man daga baya ne suka kulle saboda tashin farashi.
Wani mai siyar da mai mai suna Abdulmajid Muhammad ya tabbatar da cewa sun siyar da litar kan N970.
Ya ce daga bisani an kulle gidan man inda ya ce akwai hasashen gobe za su fara siyarwa kan N1,200 ko fiye da haka.
Matatar Dangote ta fara samar da fetur
A wani labarin, kun ji cewa matatar man attajiri Aliko Dangote ta bayyana tsarin yadda za ta siyar da fetur ga 'yan kasuwa.
Matatar ta tabbatar da cewa za ta fitar man kasashen ketare idan har 'yan kasuwa daga Najeriya suka ki siyan man.
Mataimakin shugaban bangaren man da kuma gas, Devakumar Edwin shi ya bayyana haka a jiya Litinin 2 ga watan Satumbar 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng