Muhimman Abubuwa 7 da Dangote Ya Fada yayin Fara Fitar da Man Fetur a Matatarsa

Muhimman Abubuwa 7 da Dangote Ya Fada yayin Fara Fitar da Man Fetur a Matatarsa

  • A yau shahararren mai kudin Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya fara fitar da tataccen man fetur daga matatarsa da ke jihar Legas
  • Alhaji Aliko Dangote ya yi jawabi na musamman ga al'ummar duniya yayin da ya kafa tarihin fara tace man fetur a Najeriya
  • A wannan rahoton, Legit ta tatttaro muku wasu daga cikin muhimman abubuwa da Aliko Dangote ya fada cikin jawabinsa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas - Shahararren mai kudin Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya fara fitar da man fetur a matatar mai da ya gina a Legas.

Alhaji Aliko Dangote ya yi jawabi na musamman ga yan Najeriya da al'ummar duniya yayin fara fitar da man fetur da ya tace.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban ƙasa ta yi maganar man fetur ana tsaka da wahala a Najeriya

Matatar Dangote
Matatar dangote za ta wadata Najeriya da man fetur. Hoto: Dangote Industries
Asali: UGC

A wannan rahoton, mun tattaro muku wasu daga cikin abubuwa masu muhimmanci da Dangote ya fada yayin hira da manema labarai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abubuwa 7 da Dangote ya fada a matatarsa

  1. Aliko Dangote ya ce fara fitar da mai daga matatarsa zai kawo karshen dogayen layuka a gidajen man Najeriya da ake fama da su tsawon shekaru.
  2. Dan kasuwar ya bayyana cewa fitar da man fetur daga matatarsa zai nuna ainihin man fetur da ake amfani da shi a Najeriya domin ya samar da na'urar ƙididdiga.
  3. Dangote ya bayyana cewa a yau Talata, 3 ga watan Satumba ya fara fitar da man fetur a matatarsa ta Legas.
  4. Haka zalika Aliko Dangote ya bayyana cewa samar da mai daga matatarsa zai rage buƙatar dala da kashi 40% a Najeriya.
  5. Rahoton Channels Television ya nuna cewa Dangote ya bayyana cewa injunan motocin Najeriya za su kara inganci saboda yana fitar da mai ne mai matuƙar kyau.
  6. The Cable ta wallafa cewa shahararren dan kasuwar ya ce man fetur dinsa na daidai ta wajen inganci da dukkan man fetur a fadin duniya.
  7. A karshe, Dangote ya ce nan da awa 48 za su fara fitar da man fetur zuwa ga kamfanin NNPCL domin raba shi ga yan kasuwa.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta bayyana adadin litar fetur da matatar Dangote za ta rika samarwa a kullum

Farashin man fetur ya tashi a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Bola Tinubu ta barranta kanta daga rahoton da ke cewa ta ba NNPCL umarnin sayar da fetur kan sabon farashi.

An samu bullar labarin cewa Ministan albarkatun man fetur, Heineken Lokpobiri ya umarci NNPCL ya sayar da fetur kan sama da N1000.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng