"Ku Kwana da Shiri," 'Yan Kasuwa Sun Yi Barazanar Karuwar Farashin Litar Fetur

"Ku Kwana da Shiri," 'Yan Kasuwa Sun Yi Barazanar Karuwar Farashin Litar Fetur

  • Yan kasuwar fetur sun yi barazanar cewa za a samu karuwar farashin man fetur nan ba da jimawa ba a Najeriya
  • Gargadin yan kasuwan na zuwa ne duk da yunkurin fara sayar da man fetur daga matatar mai ta Dangote ta da fara aiki
  • 'Yan kasuwar sun gargadi yan Najeriya cewa kamfanin NNPCL ba zai iya ci gaba da sayar da fetur a kan N600 ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Shugaban kungiyar masu kasuwancin man fetur na kasa, Billy Gilly Harry ya yi gargadin cewa za a iya samun karuwar farashin litar man fetur a kasar nan.

Kara karanta wannan

Ana murna matatar Dangote ta fara samar da fetur, NNPCL ya kara farashin litar mai

Ya bayyana haka ne duk da cewa matatar kamfanin Dangote ta fara fitar da man fetur, wanda aka tace a matatar man da ke Legas.

Fetur
Yan kasuwa sun ce za a kara farashin fetur Hoto: Sefjamil Kabo
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa Mista Billy Gilly Harry ya ce kamfanin mai na kasa (NNPCL) ba zai iya ci gaba da samar da fetur da 'yan kasar nan a kan N600 kowace lita.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Dole farashin fetur ya karu" - Yan kasuwa

Shugaban kungiyar masu kasuwancin fetur a kasar nan, Billy Gilly Harry ya gargadi yan Najeriya kan su kwana cikin shirin sayen litar fetur a arashi mai tsada.

Mista Harry ya ce lokaci ya yi da za a bar mayar da batun farashin fetur siyasa, a kuma shirya sayen fetur din da tsada, Channels Television ta wallafa.

Yan kasuwa na son warware matsalar fetur

Mista Harry ya bayyana cewa kungiyoyin sayar da man fetur na kokarin nemo hanyoyin warware matsalolin da suka dabaibaye fetur a kasa.

Kara karanta wannan

Babu Najeriya: Jerin kasashe 10 na duniya da suka fi tsadar fetur a 2024

Ya bayyana cewa yanzu haka kamfanin NNPCL na fuskantar kalubale wajen wadata kasar nan da man fetur.

Gwamnati ta musanta umarnin kara farashin fetur

A baya kun ji cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta musanta cewa ta bayar da umarnin ga kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya kara farashin litar mai da ya ke sayarwa jama'a.

Ma'aikatar albarkatun fetur a karkashin Minista Heineken Lokpobiri ta ce gwamnatin tarayya ba ta da hurumin yi wa kamfanin NNPCL katsalandan a kan yadda ya ke gudanar da aikinsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.