Tsohon Dan Sanda Ya Fallasa Dalilin Gaza Kama Yan Bindiga Masu Kira Ta Waya

Tsohon Dan Sanda Ya Fallasa Dalilin Gaza Kama Yan Bindiga Masu Kira Ta Waya

  • Wani babban tsohon dan sanda ya fadi babban abin da yasa aka gaza samun nasara kan yan bindiga a Najeriya
  • Tsohon dan sandan ya fadi tsarin da tsohon sufeton 'yan sanda, Solomon Arase ya kawo domin maganin yan bindiga
  • Ya ce tsarin ya jawo an kama masu garkuwa da mutane da dama kafin rundunar yan sandan Najeriya ta watsar da shi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Wani tsohon dan sanda ya fadi dalilin da yasa ake gaza kama yan bindiga da suke kira ta waya idan sun yi garkuwa da mutane.

Tsohon dan sandan ya bayyana cewa a baya akwai na'urorin da ake amfani da su wajen cafke masu garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

An fara shari'ar masu zanga zanga, za su iya fuskantar hukuncin kisa a kotu

Yan sanda
Tsohon dan sanda ya yi magana kan yan bindiga masu kira a waya. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Rahoton Vanguard ya nuna tsohon dan sandan ya zargi yan siyasa da karkatar da na'urar ƙididdigar zuwa amfaninsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Samar da na'urar ƙididdigar yan bindiga

Wani dan sanda ya bayyana cewa a lokacin sufeton yan sanda, Solomon Arase aka samar da na'urar ƙididdigar yan bindiga masu garkuwa da mutane.

Ya ce na'urar ƙididdigar ta taimakawa yan sanda wajen gano yadda masu garkuwa da mutane ke amfani da waya domin neman kudin fansa.

A cewarsa, wajen amfani da na'urar ne aka kama wadanda suka yi garkuwa da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Cif Olu Falae a 2015.

An yi watsi da na'urar ƙididdigar yan bindiga

Tsohon dan sandar ya ce shugabannin yan sanda da suka biyo baya ba su yi amfani da na'urar yadda ya kamata ba.

Ya yi zargin cewa yan siyasar Najeriya ne suka karkatar da na'urar domin amfaninsu wajen kididdigar yan adawa maimakon yan bindiga.

Kara karanta wannan

Kisan gilla: 'Yan sanda sun tono gawar 'yan banga, an kama basarake

Ana cikin haka ne kuma a cewarsa har aka kai matakin da na'urar ƙididdigar ta daina aiki kwata kwata a Najeriya inda yan bindiga ke cin karensu babu babbaka.

IGP ya dawo da na'urar ƙididdiga

Sai dai jaridar Daily Trust ta wallafa cewa sufeton yan sanda, IGP Kayode Egbetokun ya dawo da na'urar domin fara aiki.

Amma duk da haka masu garkuwa da mutane suna cigaba da kiran waya suna karbar kudin fansa a Najeriya a lokuta daban daban.

An kwace bindigar NDLEA a Bayelsa

A wani rahoton, kun ji cewa rahotanni da suka fito daga Bayelsa sun yi nuni da cewa wasu matasa sun tare jami'an hukumar yaki da shan miyagun kwayoyi.

An ruwaito cewa bata garin matasan sun kwace bindigar da wani jami'in NDLEA yake rike da ita kuma suka harbi jami'an da bindigar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng