Daga Ƙarshe, Matatar Ɗangote Ta Gabatar da Sumfurin Farko na Fetur Ɗinta a Najeriya

Daga Ƙarshe, Matatar Ɗangote Ta Gabatar da Sumfurin Farko na Fetur Ɗinta a Najeriya

  • Matatar man Ɗangote ta gabatar da sumfurin farko na fetur ɗin da ta tace wanda zai shiga kasuwa nan gaba kaɗan
  • Alhaji Aliko Ɗangote shi ya bayyana sumfurin yayin zantawa da ƴan jarida ranar Talata da safe a matatar da ke Legas
  • Hamsashaƙin ɗan kasuwar ya godewa ƴan Najeriya da Bola Ahmed Tinubu bisa goyon bayan da suka ba matatarsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Matatar man fetur ta attajirin ɗan kasuwar nan, Alhaji Aliko Ɗangote ta fitar da sumfurin farko na man fetur ɗinta da zai shiga kasuwa nan ba da daɗewa ba.

Shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote Group, Aliko Ɗangote, shi ne ya nuna sumfurin da safiyar yau Talata, 3 ga watan Satumba, 2024.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban ƙasa ta yi maganar man fetur ana tsaka da wahala a Najeriya

Aliko Dangote.
Sumfurin man fetur na farko daga matatar Dangote ya bayyana Hoto: Alhaji Aliko Ɗangote
Asali: Getty Images

Matatar Ɗangote ta gabatar da sumfurin farko

Hamshaƙin attajirin ya bayyana sumfurin ne a wani jawabi da ya yi kai tsaye a matatar man da ke jihar Legas, in ji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan ba ku manta a ƴan makonnin da suka shige, matatar mai ƙarfin ɗaukar ganguna 650,000 ta fara gwaji gabanin fara fitar da man fetur zuwa kasuwa.

Ɗangote ya godewa Tinubu da ƴan Najeriya

A jawabinsa, Ɗangote ya ce:

"Ina mai jinjinawa ɗaukacin ƴan Najeriya da gwamnatin tarayya ƙarƙashin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu bisa yadda suka ba mu goyon baya muka kawo wannan mataki.
"Ina kuma ƙara miƙa godiya ta musamman ga shugaban ƙasa bisa amincewa da tsarin sayar da mai da kuɗinmu na gida Najeriya, hakan zai daidaita farashin Naira.
"A yanzu da wannan matatar ta fara aiki, za mu san ainihin adadin man fetur ɗin da Najeriya take buƙata, za mu iya bin diddigin kowace mota da jirgin ruwa."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun jefa bama bamai a hedkwatar ƴan sanda, sun tafka ta'asa

Ɗangote ya ƙara da cewa matatar man da ya gina za ta samar da isashen fetur da ƴan Najeriya ke bukata har a fitar da shi zuwa ƙasashen nahiyar Afirka, The Nation ta kawo labarin.

Gwamnatin Tinubu ta ƙara farashin fetur?

A wani rahoton kuma Gwamnatin Bola Tinubu ta barranta kanta daga rahoton da ke cewa ta ba kamfanin NNPCL umarnin sayar da fetur kan sabon farashi

An samu bullar labarin cewa Ministan albarkatun man fetur, Heineken Lokpobiri ya umarci NNPCL ya sayar da fetur kan sama da N1000.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262