Bayan Karbe Kudin Fansa N17m, Miyagu Sun Saba Alkawari, Sun Kashe 'Dan Shekara 19
- Wasu azzaluman masu garkuwa da mutane sun hallaka matashi dan shekara 19 a karamar hukumar Lafia da ke Nasarawa
- Miyagun sun sace matashin mai suna Anas Zubairu bayan ya dawo hutun makaranta daga kasar Morocco inda ya ke karatu
- Miyagun sun sace shi har gida a lokacin da ya ke kokarin rufe kofa bayan ya ajiye motar sa, sai suka harbe shi a kafadarsa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Nasarawa - Wasu masu garkuwa da mutane sun nuna rashin imaninsu inda su ka kashe matashi mai shekaru 19, Anas Zubairu.
Miyagun sun kama matashin ne da yammacin Juma'a jim kadan bayan ya dawo gida daga Morocco inda ya ke karatu a jami'o'in kasar.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa bayan Anas ya ajiye mota zai je rufe kofar gidansu ne miyagun su ka harbe shi a kafada, sannan su ka yi awon gaba da shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwanaki biyar bayan sace matashin ne miyagun su ka nemi kudin fansar N30m daga yan uwansa gabanin a sake shi.
Miyagu sun ci kudin fansa, sun kashe shi
Masu garkuwa da mutane sun kashe Anas Zubairu bayan yan uwansa sun biya kudin fansa na N17m da niyyar za a sako ma su shi.
Politics Nigeria ta wallafa cewa tsohuwar kwamishinar mata a jihar Nasarawa, Halima Jabiru wacce ammi ce ga marigayin ta tabbatar da hakan.
Martanin yan sanda kan aikin miyagun
'Yan uwan Anas sun ce miyagun sun shaida ma su rasuwar dan su kwanaki biyu bayan karbar kudin fansa daga yan uwansa.
Amma rundunar yan sandan jihar ta bayyana cewa ba ta da masaniyar sace matashin ko kashe da miyagu su ka yi.
Dakarun sojoji sun kashe miyagu
A baya mun ruwaito cewa dakarun rundunar sojojin saman kasar nan sun hallaka fitinannen dan ta'adda da ya addabi jama'a a jihar Kaduna bayan sun sha aman wuta ta sama.
A luguden wutar da su ka yi, dakarun sun yi nasarar sheke jagoran yan ta'addan, Mustapha Abdullahi da sauran yaransa guda biyar a karamar hukumar Igabi a jihar
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng