Tinubu Ya Kadu da Rasuwar Mahaifiyar Yar’Adua, Ya Fadi Alherin da Ta Shuka
- Shugaban kasa, Bola Tinubu ya kadu bayan samun labarin rasuwar mahaifiyar marigayi tsohon shugaban kasa, Umaru Musa Yar'Adua
- Tinubu ya tura sakon ta'aziyya ga iyalan marigayiyar inda ya ce tabbas an yi babban rashin da zai wahala a taba mantawa da ita
- Hakan ya biyo bayan rasuwar Hajiya Dada wacce ta cika a ranar Litinin 2 ga watan Satumbar 2024 a asibitin koyon aiki a Katsina
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya tura sakon ta'aziyya ga iyalan marigayiya Hajiya Dada a jihar Katsina.
Tinubu ya ce tabbas rasa Hajiya Dada babban rashi ne ga al'umma inda ya yaba da gudunmawar da ta bayar.
Tinubu ya yi ta'aziyyar rasuwar Dada Yar'Adua
Hadimin shugaban, Ajuri Ngelale shi ya bayyana haka a shafinsa na Facebook a yau Talata 3 ga watan Satumbar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce Tinubu ya kuma tura sakon ta'aziyya ga Sanata Abdul'aziz Musa Yar'Adua da al'ummar jihar Katsina.
Tinubu ya ce tabbas marigayiyar ta taba rayuwar al'umma da dama wanda ba za a taba mantawa da hakan ba.
Tinubu ya fadi alherin Dada Yar'Adua
"Ina amfanin da wannan dama domin tura sakon ta'aziyya ga Sanata Abdul'aziz Musa Yar'Adua da mutanen jihar Katsina da kuma mutanen da dattijuwar ta taba rayuwarsu."
"Tabbas an yi rashi game da mutuwar marigayiyar tare da alhini kan rashin da aka yi na mata mai tausayi gaskiya da kuma mu'amala mai kyau."
"Ina addu'ar Allah ya yi mata rahama ya kuma albarkaci bayanta, tabbas ba za a taba mantawa da ita ba saboda goyon baya da sanya farin ciki da ta yi ga al'umma."
- Bola Tinubu
Dada Yar'Adua ta haifi manya
Wannan na zuwa ne bayan rasuwar Hajiya Dada a jiya Litinin 2 ga watan Satumbar 2024 a asibitin Tarayya da ke Katsina tana da shekaru 102.
Daga cikin 'ya'yanta akwai wanda ya rike shugabancin kasa da gwamnan jiha har sau biyu watau marigayi Ummaru Yar'adua.
Sannan akwai mataimakin shugaban kasa da Minista da Sanata da Manjo-janar da Kanal na soja da sauransu.
Mahaifiyar marigayi Yar'Adua ta rasu
Kun ji cewa mahaifiyar tsohon shugaban ƙasa, Marigayi Umaru Musa Yar'adua, Hajiya Dada ta riga mu gidan gaskiya a jihar Ƙatsina.
Rahotanni sun nuna cewa Hajiya Dada ta rasu ne bayan fama da rashin lafiya a jiya Litinin 2 ga watan Satumba 2024, tana da shekaru 102.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng