"Rudewa Suka Yi," Bature Ya Yi Martani kan Zargin Yunkurin Kifar da Gwamnatin Tinubu

"Rudewa Suka Yi," Bature Ya Yi Martani kan Zargin Yunkurin Kifar da Gwamnatin Tinubu

  • Andrew Wynne, dan kasar Burtaniya da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta zarga da kokarin kifar da ita ya musanta zargin
  • Mista Wynne ya bayyana cewa bai ma san ana neman shi ruwa a jallo bisa zargin yunkurin kawo sauyin gwamnati a Najeriya ba
  • Martanin baturen na zuwa bayan rundunar yan sandan kasar nan ta sanya kyautar N20m kan wanda ya kawo ma ta shi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Andrew Wynne, dan kasar Burtaniya da rundunar yan sandan kasar nan ta ce ta na nema ruwa a jallo ya musanta zargin da hukumomin Najeriya ke yi masa.

Kara karanta wannan

"Akwai jan aiki a gaba": Yadda 'yan Najeriya za su magance matsalolin kasar da kansu

Mista Wynne ya ce ba shi da masaniya kan zargin kokarin kifar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu a lokacin zanga-zangar adawa da yunwa.

Andrew
Dan Burtaniya ya musanta hannu a yunkurin kifar da gwamnatin Tinubu Hoto: Ajuri Ngelale/Elelu Ayoola
Asali: Facebook

Channels Television ta wallafa cewa Andrew Wynne ya ce ba shi da masaniyar Najeriya ta makala masa sunan mai laifi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Martaninsa na zuwa ne awannin kadan bayan bayyana shi a matsayin mai laifi tare da sanya N20m ga duk wanda ya kawo shi da wani dan asalin kasar nan, Lucky Obiyan.

"Gwamnatin Najeriya ta tsorata," Andrew Wynne

Dan kasar Burtaniya da ake zargi da kokarin daukar nauyin masu kifar da gwamnatin Tinubu, Andrew Wynne ya ce zanga-zanga ta tsorata gwamnati ne kawai.

Jaridar Punch ta wallafa cewa Mista Andrew ya ce ya shafe shekaru 25 ya na shigowa Najeriya, kuma ya na da ofishi a cikin hedkwatar NLC a Abuja.

Kara karanta wannan

Mata sun zargi rundunar sojojin kasa, sun nemi a janye dakaru daga yankin Ibo

Wynne zai yi bayani ga gwamnatin Najeriya

Mista Andrew Wynne ya bayyana cewa ba guduwa kasar sa ya yi ba biyo bayan bincike da gwamnatin Najeriya ta fara kan zargin kifar da ita.

Mista Wynne ya ce a shirye ya ke da yin bayani ga hukumomin Najeriya da ke kasar Burtaniya kan zarge-zargen da ake yi masa.

Tinubu: Gwamnati na neman Andrew Wynne

A baya mun ruwaito cewa gwamnatin kasar nan ta bayyana neman wani dan Burtaniya, Andrew Wynne bisa zargin hannu cikin kokarin kifar da gwamnati.

Rundunar yan sandan kasar ta ce ana zargin Wynne da daukar nauyin yadda za a kifar da gwamnatin Tinubu a lokacin zanga-zangar yunwa da aka yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.