Asiri Ya Tonu: Gwamnatin Kano Ta Kama 'Hedimasta' da Zargin Saida Kayan Makaranta

Asiri Ya Tonu: Gwamnatin Kano Ta Kama 'Hedimasta' da Zargin Saida Kayan Makaranta

  • Gwamnatin Kano ta cafke wani shugaban makarantar firamare bisa zargin cefanar da wasu cikin kayan da aka zuba a makarantar
  • Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa (PCACC) ce ta kama malamin makarantar firamaren Gaidar Makada
  • Duk da ba a bayyana sunan shugaban makarantar ba, hukumar yaki da rashawa ta ce an kai ga gano wasu daga kayan da aka dauke

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta damke shugaban makarantar firamaren Gaidar Makada da ke karamar hukumar Kumbotso da ke Kano.

Ana zargin shugaban firamaren ne bayan wasu daga cikin kayan makarantar sun fara bacewa daya bayan daya, lamarin da ya sa aka ankarar da mahukunta.

Kara karanta wannan

An fara shari'ar masu zanga zanga, za su iya fuskantar hukuncin kisa a kotu

Rashawa
An damke malamin makaranta kan sayar da kayan makaranta a Kano Hoto: Abubakar Dahiru Yakasai
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa a sanarwar da jami'in hulda da jama'a na hukumar PCACC, Kabir Abba Kabir ya fitar, hukumarsu ta shiga bincike bayan samun korafin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta kara da cewa an kai ga gano wasu daga cikin kayan makarantar da wanda ake zargi tsaye kansu.

Kano: Yadda aka kama malamin a makaranta

Jaridar Punch ta wallafa cewa hukumar karbar korafe-korafe da yaki da rashawa ta jihar Kano ta damke malami da wasu mutane uku bisa kokarin sayar da kayan makaranta.

Mazauna yankin ne su ka ji wani motsi da ba su gamsu da shi ba daga cikin firamaren Gaidar Makada a ranar Asabar, inda su ka matsa domin ganin dalili.

A nan ne aka ga shugaban makarantar da wasu ana tsaka da cinikin kayan karatun dalibai, daga cikin har da kujeru, kofofi da wasu kayan makarantar.

Kara karanta wannan

Gobara ta tashi a gidan gwamnatin Katsina, ta shafi bangaren ofishin gwamna

Malamin makaranta ya rasu a Kano

A wani rahoton kun ji cewa Farfesa mai matsalar gani na farko a Najeriya, Jibril Isa Diso ya koma ga mahallicinsa bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Jami'ar Bayero da ke Kano ta fitar da sanarwar rasuwar Farfesan a ranar Juma'a, lamarin da ya jawo zaman alhini musamman a wajen dalibansa da su ka yaba da yadda ya taimake su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.