'Yan bindiga Sun Kai Mummunan Hari kan Matafiya, Sun Tafka Ɓarna a Arewa
- Yan bindiga sun jikkata mafarauta da suka kai hari titin Takete Ide a karamar hukumar Mupamuro da ke jihar Kogi
- Rahoto ya nuna maharan sun tare matafiya, kuma sun kwace masu kuɗi da kayayyaki masu daraja a harin na ranar Lahadi
- Gwamnatin Kogi ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce tuni Gwamma Ahmed Ododo ya fara ɗaukar matakan da suka dace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kogi - Wasu ‘yan bindiga dauke da mugayen makamai sun kai wa matafiya hari a kan titin Takete Ide zuwa Aghara a jihar Kogi.
Rahotanni sun nuna maharan sun jikkata mutane da dama a harin tare da kwace masu dukiyoyi da kayayyaki masu daraja da tsada.
Leadership ta tattaro cewa ƴan bindigar ɗauke da bindigun AK-47 sun tare hanyar tun da tsakar rana har zuwa yamma, inda suka yi wa matafiya ɓarna mai yawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga sun yi wa matafiya tatas
Bayanai sun nuna cewa ɓarayin sun tsayar da matafiya masu yawa, kana suka kwace masu dukiya, wanda ya yi kunnen ƙashi kuma suka azabtar da shi a wuri .
Mazauna garin Takete Ide da ke ƙaramar hukumar Mopamuro a Kogi sun yi kokarin hana maharan shiga yankinsu bayan samun bayanan sirri.
Da farko mafarauta sun kama hanyar zuwa kai ɗauki kam titin, amma kafin su karisa ɓarayin suka canza wuri, suka ƙara matsawa kusa da garin Takete-Ide.
Mafarauta sun yi musayar wuta da 'yan bindiga
A cewar wata majiya, ƴan bindigar sun yi wa mafarautan kwantan bauta, inda aka yi musayar wuta mai zafi a tsakaninsu.
Mutum uku daga cikin mafarautan sun samu raunuka yayin da ɗaya kuma ya ɓata ba a sake ganinsa ba sai da safiyar ranar Litinin, cewar rahoton Daily Post.
Wannan hari dai ya jawo tsoro da firgici a zukatan mazauna garin waɗanda galibi ba su iya barci ba a daren saboda gudun abin da ka iya zuwa ya dawo.
Gwamnatin Kogi ta ɗauki mataki
Da yake mayar da martani kan lamarin, kwamishinan yada labarai na jihar Kogi, Kingsley Fanwo, ya ce gwamnati ta samu labari kuma tuni aka fara ɗaukar mataki.
"Mun samu labarin harin da aka kai Mupamoro kuma tuni gwamna ya ɗauki mataki domin shawo kan lamarin da kuma kamo masu hannu don a hukunta su," in ji shi.
Sojoji sun murkushe ƴan bindiga a Kaduna
A wani labarin na daban sojojin Najeriya sun hallaka ƴan bindigar daji takwas a yankin ƙaramar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna
Gwamnatin Kaduna ta ce sojojin sun sheƙe ƴan ta'addar ne a lokacin da suka fita sintiri a kewayen Kamfanin Doka da Gayam.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng