Kotu Ta Dauki Mataki kan Masu Zanga Zanga da Aka Fara Shari'arsu

Kotu Ta Dauki Mataki kan Masu Zanga Zanga da Aka Fara Shari'arsu

  • Babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta fara sauraron shari'ar masu zanga-zanga da aka gurfanar
  • Alƙalin kotun mai shari'a, Emeka Nwete, ya umarci a tsare masu zanga-zangar su 10 a gidajen gyaran halin na Kuje da Suleja
  • Mai shari'a Emeka Nwite ya kuma sanya ranar, 11 ga watan Satumba domin yin hukunci kan buƙatar neman belin nasu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare wasu masu zanga-zangar #EndBadGovernance guda 10 a gidan yari.

Kotun ta bayar da umarnin tsare masu zanga-zangar ne a ranar Litinin, 2 ga watan Satumban 2024.

Kotu ta tsare masu zanga-zanga
Kotu ta tura masu zanga-zanga zuwa gidan gyaran hali Hoto: PIERRE FAVENNEC/AFP
Asali: Facebook

Kotu ta umarci tsare masu zanga - zanga

Kara karanta wannan

Aisha Abdulkarim: Kotu ta rufe asusu 20 na wata mata da ake zargi da ta'addanci a Najeriya

Jaridar Daily Trust ta ce mai shari’a Emeka Nwite ya bayar da umarnin tsare maza mutum tara daga cikinsu a gidan gyaran hali na Kuje, yayin da ya umarci a tsare mace ɗaya daga cikinsu a gidan gyaran hali na Suleja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama masu zanga-zangar ne biyo bayan zanga-zangar da aka yi a faɗin ƙasar nan a ranakun 1 zuwa 10 ga watan Agusta na nuna adawa da wahalhalun da da ake sha a ƙasa.

Kotun ta kuma sanya ranar 11 ga watan Satumba domin yin hukunci kan buƙatar neman belin da masu zanga-zangar suka yi, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.

Mutanen da aka tura gidan gyaran hali

Mutane 10 da aka gurfanar sun haɗa da Michael Adaramoye wanda aka fi sani da Lenin, Adeyemi Abayomi, Suleiman Yakubu, Opaoluwa Simon da Angel Innocent.

Kara karanta wannan

Masu zanga zangar da aka kama sun fusata, sun tura zazzafan saƙo ga Tinubu

Sauran sun haɗa da Buhari Lawal, Mosiu Sadiq, Bashir Bello, Nuradeen Khamis,da kuma Abdulsalam Zubairu.

Masu zanga-zanga sun caccaki Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa matasan da jami'an tsaron Najeriya suka cafke a lokacin zanga-zangar yunwa sun yi fatali da umarnin kotu na ci gaba da tsare su.

Sun shaidawa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu cewa ba shi da hurumin kama su, musamman saboda yana daya daga cikin waɗanda suka fi amfana da zanga-zanga.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng