Gwamna Abba Gida Gida Ya Fusata da Aiki, Ya Kwace Kwangilar Titi a Kano

Gwamna Abba Gida Gida Ya Fusata da Aiki, Ya Kwace Kwangilar Titi a Kano

  • Mai girma Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya kwace kwangilar gina titi a karamar hukumar Garko saboda wasu matsaloli
  • Gwamnan ya bayyana matakin ne jim kadan bayan kaddamar da wani aikin noman rani na Kafinchiri na Naira Biliyan 2.5
  • Abba ya zargi dan kwangilar da wasa da aiki, inda ya bayyana cewa za a nemi wani mai rikon amana domin ci gaba da aikin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana takaicin yadda aikin titin Garko ke tafiyar hawainiya, lamarin da ya sa shi daukar mataki.

Gwamna Abba ya kwace kwangilar aikin titin daga wanda aka ba ya yi tun da fari, inda ya zargi kamfanin da kin komawa kan titin domin karasa aikin da aka fara.

Kara karanta wannan

Gina gidaje 500 a Kano: Dan kwangila ya harzuka minista, an gindaya masa sharuda

Abba Kabir
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karbe kwangilar aikin titi Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa gwamnan ya ce nan da wasu kwanaki za a sake bayar da kwangilar titin ga wani dan kwagila mai rikon amana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka kuma ya yiwa al'umar karamar hukumar Garko alkawarin gina masu asibiti na zamani domin inganta lafiyar mazauna kauyen.

Abba Gida Gida ya kaddamar da aiki a Garko

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya duba yadda aikin samar da wurin aikin noman rani da Kafinchiri dake gudana a karamar hukumar Garko ke tafiya.

Aikin, ya kai N2.5bn, kuma gwamna Abba ya ce ana sa ran kammaluwarsa zai habaka noman rani domin inganta abinci a jihar.

A sanarwar da darakta kan yada labaran gwamna, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, gwamna Abba ya ce aikin na daga cikin kokarin gwamnatinsa na habaka noma.

Kara karanta wannan

Abba ya sa tsoho sharba kuka a gidan gwamnati, Allah ya amsa addu’ar dattijo

Abba Gida Gida zai karasa aikin Kwankwaso

A wani labarin kun ji cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta karasa aikin titin da tsohon gwamnan jihar, Rabi'u Musa Kwankwaso ya fara.

Gwamna Abba ya bayyana takaicin yadda dan kwangilar aikin titin Kunci da ke karamar hukumar Ghari ya yi wasarere da aiki, inda ya yi barazanar kwace aikin daga hannunsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.