'Yan Bindiga Sun Hallaka Jami'an Tsaro yayin Wani Farmaki a Sokoto
- Ƴan bindiga sun kai hari kan jami'an ƴan sanda a wani shingen bincike da ke jihar Sokoto a yankin Arewa maso Yamma
- Miyagun ƴan bindigan sun hallaka ɗan sanda ɗaya tare da wani ɗan banga bayan sun shammace su a shingen binciken
- Wani babban jami'in ƴan sanda da ya tabbatar da aukuwar lamarin ya bayyana cewa an kai gawarwarkin ɗakin ajiya gawa da ke asibitin koyarwa na UDUTH
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - Ƴan bindiga sun kashe ɗan sanda ɗaya da wani ɗan banga da ke sintiri a jihar Sokoto.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3:00 na safiyar ranar Litinin a Kwanan Milgoma da ke kan titin Sokoto zuwa Bodinga.
Yadda ƴan bindiga suka kai harin
Wani babban jami’in ƴan sandan da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatarwa jaridar Daily Trust aukuwar harin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa ƴan bindigan sun mamayi jami'an tsaron ne bayan sun zo a cikin wata farar mota ƙirar Hilux.
"Ƴan bindigan sun haɗu da ƴan sandan ne a wani shingen bincike da ke kan hanyar Sokoto zuwa Bodinga inda suka buɗe musu wuta."
"Sun kashe ɗan sanda ɗaya da ɗan banga sannan suka tafi da bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu."
"An ajiye gawarwakinsu a ɗakin ajiye gawa na asibitin koyarwa na jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto."
- Wani jami'in ƴan sanda
Me kakakin rundunar ƴan sanda ya ce?
Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Sokoto, ASP Ahmad Rufa'i domin samun ƙarin bayani kan lamarin.
Kakakin ƴan sandan ya bayyana cewa yana wani abu ne a halin yanzu amma zai kira daga.
"Ina wani abu ne a halin yanzu, zan kira ka."
ASP Ahmad Rufa'i
Sai dai har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton bai kira ba.
Gwamna ya yi gargaɗi kan ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto ya gargaɗi mutane ko ƙungiyoyi da su daina siyasantar da matsalar tsaro a jihar.
Gargaɗin na gwamnan na zuwa ne yayin da matsalar tsaro a jihar ke ƙara taɓarɓarewa sakamakon ayyukan ƴan bindiga.
Asali: Legit.ng