An Fara Shari'ar Masu Zanga Zanga, Za Su Iya Fuskantar Hukuncin Kisa a Kotu
- A yau aka fara sauraren shari'ar masu zanga-zangar adawa da yunwa bayan rundunar yan sanda ta zarge su da cin amanar kasa
- Ana shari'ar mutanen da aka kamo daga jihohin Kano da Kaduna da Gombe da birnin Abuja bisa zargin yunkurin kifar da gwamnati
- Zarge-zargen da ake yi wa matasan da su ka hada da cin amanar kasa, yunkurin kawo sauyin gwamnati da tayar da zaune tsaye na dauke da hukuncin kisa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - A yanzu haka ana can an fara sauraren shari'ar matasan da rundunar yan sandan kasar nan ta kama a lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa.
Gwamnatin tarayya ta gurfanar da matasan da aka kamo daga jihohin Kaduna, Kano, Gombe da Abuja a gaban babbar kotu da ke Abuja.
Jaridar Punch ta wallafa cewa an kawo wadanda ake zargi gaban kotu a cikin tsauraran matakan tsaro inda ake tuhumarsy da cin amanar kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran zarge zargen sun hada da kokarin kawo sauyin gwamnati da tayar da tarzoma, kuma tuhume-tuhumen ka iya fuskantar hukuncin kisa.
Zanga-zanga: An gurfanar da matasa kotu
Channels Television ta wallafa cewa gwamnatin tarayya ta gurfanar da masu zanga zanga a kasar nan 10 a gaban alkalin kotun tarayya Abuja, Mai Shari'a Emeka Nwite.
Matasan da aka gurfanar sun hada da Michael Tobiloba Adaramoye, Adeyemi Abiodun Abayomi, Suleiman Yakubu, Comrade Opaluwa Eleojo Simeon, Angel Innocent da Buhari Lawal.
Sauran sun hada da Mosiu Sadiq; Bashir Bello, Nuradeen Khamis da Abdulsalam Zubairu, kuma ana zarginsu da jawo tashin hankali a kasar nan.
Masu zanga zanga sun kai kara kotu
A baya mun ruwaito cewa wasu daga cikin wadanda gwamnatin kasar nan ta kama bisa gudanar da zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin Bola Tinubu sun fusata kan tsare da su da aka yi.
Matasan sun shigar da gwamnatin tarayya gaban kotu, inda suka bayyana cewa gwamnatin ba ta da hurumin tsare su har na kwanaki sama da 60 ba tare da an mika su gaban kotu ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng