Daga Karshe an Sanya Lokacin Fara Sayar da Man Fetur Na Matatar Dangote a Kasuwa

Daga Karshe an Sanya Lokacin Fara Sayar da Man Fetur Na Matatar Dangote a Kasuwa

  • Abin da aka daɗe ana jira dangane da matatar man hamsahaƙin attajirin nan Alhaji Aliko Dangote, ya kusa tabbata
  • Matatar man ta Dangote ta shirya fara sayar da man fetur wanda ta tace a kasuwannin Najeriya nan ba da jimawa ba
  • Majiyoyin sun tabbatar da cewa kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) ne zai riƙa sayar da man Dangote a halin yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Matatar man Dangote wacce ke a jihar Legas za ta fara siyar da man fetur a kasuwa.

Hakan na zuwa ne zuwa ne ƴan kwanaki kaɗan bayan matatar wacce za ta samar da ganguna 650,000 a kullum ta fara yin gwaje-gwaje kan fitar da man fetur ɗin.

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya dauki mataki da gobara ta tashi a gidan gwamnati

Matatar Dangote ta shirya fara sayar da fetur
Matatar man Dangote za ta fara sayar da fetur Hoto: Bloomberg
Asali: Getty Images

Yaushe za a fara sayar da man a kasuwa?

Jaridar The Punch ta rahoto cewa majiyoyi sun tabbatar mata da cewa man fetur ɗin zai shigo kasuwa nan ba da jimawa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyin waɗanda suka nemi a sakaya sunansu, sun bayyana cewa gwamnati da kuma kamfanin Dangote suna tsara hanyoyin da za a rika jigilar man fetur ɗin.

Wata majiyar gwamnati ta yi nuni da cewa ana tsara yadda za a riƙa rarrabawa tare da sayar da man fetur ɗin tsakanin gwamnatin tarayya da kamfanin.

Majiyar ta ƙara da cewa kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) ne kaɗai zai iya siyar da man fetur na matatar Dangote a halin yanzu.

Matatar Dangote ta fuskanci ƙalubale

Tun a watan Yuni ne dai ya kamata a ce man fetur daga matatar Dangote ya shiga kasuwa, amma hakan bai faru ba saboda matsalolin da matatar ta fuskanta da hukumomi a Najeriya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga na kai hare hare, gwamnan Sokoto ya gargadi 'yan adawa

Sanya bakin da gwamnatin tarayya ta yi na cewa a riƙa sayar da ɗanyen mai ga matatar a Naira, da alama ya fara haifar da ɗa mai ido.

Karanta wasu labaran kan matatar Dangote

Obasanjo ya yi fallasa kan matatar Dangote

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya yi gargadin cewa masu samun arziki daga shigo da mai ba za su bari matatar man Dangote ta yi nasara ba.

Olusegun Obasanjo ya yi wannan ikirarin ne bayan da Aliko Dangote, shugaban rukunin kamfanonin Dangote ya yi zargin cewa wasu 'kusoshi' na son kawo cikas ga matatarsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng