"Muna Bukatar Juna," Ƙungiyar Arewa ta Jinjinawa Tinubu kan Sasantawa da Nijar

"Muna Bukatar Juna," Ƙungiyar Arewa ta Jinjinawa Tinubu kan Sasantawa da Nijar

  • Kungiyar ACF ta jinjinawa yadda shugaban kasa, Bola Tinubu ya sahale sojojin kasar nan su ka ziyarci Nijar domin gyara alaka tsakanin kasashen
  • A makon da ya gabata ne babban hafsan sojojin kasa, Janar Christopher Musa ya jagoranci tawaga zuwa kasar Nijar duk da takun saka da ke tsakaninsu
  • A sanarwar da ta fitar, ACF ta ce shugaba Tinubu ya yi tunani mai kyau domin kasashen na bukatar juna ta fuskokin samar da ci gaba da dama

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna - Kungiyar ACF ta jinjinawa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da ya amince tawagar sojojin kasar nan ta kai ziyarar gyara alaka jamhuriyyar Nijar.

Kara karanta wannan

Kano: Dan majalisa zai taimaki addini, ya yi kyautar miliyoyin sayen motar wa'azi

Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran kungiyar, Farfesa Tanko Muhammad Bala ya fitar a ranar Lahadi.

Bola Ahmed
Kungiyar ACF ta yaba da yadda gwamnatin Tinubu ta dauko shiri da Nijar Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa kungiyar ACF ta yaba da kalaman da Janar Christopher Musa ya yi amfani da su yayin ziyarar da ya kai kasar Nijar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nijar da Najeriya sun sabunta kawance

Kungiyar ACF ta shawarci 'yan jamhuriyyar Nijar da su yafe sabanin da kasarsu ta samu da Najeriya da sauran kasashen ECOWAS a baya.

A sanarwar da sakataren yada labaran kungiyar, Farfesa Tanko Muhammad Bala ya fitar, ya ce yanzu lokaci ne da kasashen biyu za su fara aiki tare domin cigabansu.

Najeriya da Nijar na bukatar juna

Shugaban kungiyar ACF a nan Kano, Dakta Farouq Goni ya shaidawa majiyar Legit cewa Najeriya da Nijar na bukatar juna ta fuskar kasuwanci da tsaro.

Kara karanta wannan

Atiku da Obi sun yi martani kan inyamura mai ikirarin kashe yan Najeriya a Canada

A yabon da ya yiwa shugaba Tinubu kan kyautata alaka da Nijar, Dr. Goni ya ce idan an samu dama, za su sake neman mika wasu shawarwarin ga shugaban kasa kan kasashen biyu.

Babban hafsan sojan Najeriya ya ziyarci Nijar

A baya kun ji cewa babban hafsan sojojin kasar nan, Janar Christopher Musa ya jagoranci tawagar manyan jami'an sojojin kasar nan zuwa jamhuriyyar Nijar domin kyautata alaka.

Mukaddashin daraktan yada labarai na tsaro, Birgediya Janar Tukur Gusau ya tabbatar da kai ziyarar, kuma lamarin na zuwa ne a lokacin da ake zaman doya da manja tsakanin kasashen.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.