Kano: Dan Majalisa Zai Taimaki Addini, Ya Yi Kyautar Miliyoyin Sayen Motar Da'awa

Kano: Dan Majalisa Zai Taimaki Addini, Ya Yi Kyautar Miliyoyin Sayen Motar Da'awa

  • Dan majalisar wakilai da ke wakiltar Doguwa/Tudun Wada, Alhasan Ado Doguwa ya yi kyautar miliyoyi
  • Dan majalisar da abokansa sun bayar da Naira Miliyan 7 ga kungiyar da'awar musulunci domin sayen mota
  • A jawabinsa, shugaban kungiyar ta Adyan, Abdulwakeel Abdulsalami ya shawarci matasa su zamo masu gudun duniya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Dan majalisar Kano mai wakiltar Doguwa/Tudun Wada, Hon. Alhassan Ado Doguwa ya taimakawa wajen kungiyar yada musulunci da kudin sayen mota.

Dan majalisar da abokansa sun hada Naira Miliyan 7 domin sayo mota kirar bas wacce za a rika amfani da ita wajen yada addinin Allah.

Kara karanta wannan

Miyagun ƴan bindiga sun hallaka babban hadimin shugaban majalisa a Najeriya

Alhassan
Dan majalisa a Kano ya bayar da Naira Miliyan 7 domin sayen motar da'awa Hoto: Alhassan Ado Doguwa TV
Asali: Facebook

Shafin Alhasan Ado Doguwa TV a Facebook ya wallafa cewa kungiyar ta mika lambar karramawa ga dan majalisar saboda kokarinsa wajen taimakon yada musulunci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kungiyar da'awar, AbdulWakil AbdulSalami ya bayyana cewa shirin nasu ya samu kalubale da dama bisa wasu dalilai.

Zanga-zanga ya kawo cikas ga wa'azi

AbdulSalami ya bayyana cewa tsadar rayuwa da zanga-zanga sun kawo wa shirinsu na da'awa tsaiko.

Sai dai ya shawarci matasa ka kar su bari wahalhalun rayuwar duniya su sanya su mantawa da shirin zuwa lahira, Jaridar Leadership ta wallafa.

An yi wa matasa wa'azi

Kungiyar Adyan ta shawarci matasa da su rika kula da kawunansu ganin yadda ake fama da kalubalen shaye -shaye da sauran fitintunun zamani

Shugaban kungiyar ya kuma gargadi matasa kan koyi da kafirai, domin a cewarsa hakan zai jefa rayuwarsu cikin matsala.

Kara karanta wannan

"Muna bukatar juna," Ƙungiyar Arewa ta jinjinawa Tinubu kan sasantawa da Nijar

Malami ya fusata a wajen wa'azi

A baya mun ruwaito cewa fitaccen malami, Sheikh Abubakar Umar Musa Rijiyar Lemo ya fusata yayin da ya ke kan mimbari, inda ya caccaki tikitin muslim-muslim da aka rudi yan kasa da shi.

Sheikh Abubakar Umar Musa Rijiyar Lemo ya bayyana cewa babu komai a tsarin face yaudara ganin yadda aka jefa yan Najeriya a cikin kunci da yunwa da ake fama da su a yau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.