Kano: Dan Majalisar Tarayya Ya Warkar da Makafi 3,000, Gwamna Abba Ya Yaba

Kano: Dan Majalisar Tarayya Ya Warkar da Makafi 3,000, Gwamna Abba Ya Yaba

  • Wata Gidauniya a jihar Kano ta taimakawa makafi akalla 3,000 da tiyata kyauta domin dawo musu da farin cikinsu
  • Gidauniyar Hon. Umar Datti wanda ke wakiltar Kura/Garunmallam/Madobi a Majalisar Tarayya ta yi hakan domin taimakon marasa ƙarfi
  • Kwamishinan lafiya a jihar, Dakta Abubakar Labaran Yusuf ya yabawa Gidauniyar kan irin wannan kokari da ta yi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Mutane akalla 3,000 suka ci gajiyar Gidauniyar Umar Datti a jihar Kano bayan yi musu tiyata kyauta.

Gidauniyar ta taimaki makafi da dama inda ta yi musu aiki kyauta tare da yin nasarar dawo musu da idanunsu.

Dan Majalisar Tarayya a Kano ya taimakawa marasa gani da tiyatar idanu kyauta
Dan Majalisar Tarayya, Hon. Yusuf Umar Datti ya taimakawa marasa gani da tiyatar idanu a Kano. Hoto: Rabiu Khalil Kura.
Asali: Facebook

Kano: Dan Majalisa ya taimakawa marasa ƙarfi

Kara karanta wannan

Gobara ta babbake rukunin gidajen ma'aikatan gwamnati, bayanai sun fito

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Rabiu Khalil Kura ya tabbatarwa Legit Hausa a yau Lahadi 1 ga watan Satumbar 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gidauniyar karkashin shugabancin Hon. Yusuf Umar Datti ta yi nasarar yi wa mutane 3,000 tiyatar ido ba tare da sun biya ko sisin kwabo ba.

Wadanda suka ci gajiyar sun fito ne daga mazabar dan Majalisar Tarayya, Hon. Datti Kura ta Kura/Garunmallam/Madobi da ke jihar Kano.

Gidauniyar ta dauki wannan mataki ne domin dakile matsalolin rashin samun ingantaccen kiwon lafiya musamman ga marasa karfi.

Hon. Datti ya tabbatar da himmatuwar Gidauniyar domin taimakon marasa karfi da al'ummarsu.

Gwamnatin Kano ta yabawa dan Majalisar Tarayya

A martaninsa, kwamishinan lafiya a jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf ya yabawa Gidauniyar kan wannan kokari.

Dakta Yusuf ya yabi Gidauniyar ce yayin ziyara a asibitin kwararru na Kura inda aka gudanar da aikin.

Kara karanta wannan

Kwalliya ta zo da gardama: Budurwa ta sheka lahira a wajen tiyatar karin mazaunai

Kwamishinan ya shawarci imasu hannu da shuni da 'yan siyasa da su yi koyi da wannan hobbasa na Hon. Yusuf Datti.

Wani dattijo da ya yi magana a madadin wadanda suka ci gajiyar mai suna, Abubakar Ardo Kadawa ya godewa Hon. Datti bayan shafe shekaru 10 babu idanu.

Gwamna Abba ya kaddamar da aikin hanya

Kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da aikin titin garin Kunci da ke karamar hukumar Ghari a Kano.

An fara aikin titin mai tsawon kilomita biyar tun a lokacin gwamnatin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso karo na biyu a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.