Dakarun Sojoji Sun Hallaka Kasurgumin Shugaban 'Yan Ta'adda a Arewacin Najeriya

Dakarun Sojoji Sun Hallaka Kasurgumin Shugaban 'Yan Ta'adda a Arewacin Najeriya

  • Dakarun rundunar sojojin saman Najeriya sun samu nasara kan ƴan ta'addan da suka addabi mutane a jihar Kaduna
  • Sojojin sun hallaka wani shugaban ƴan ta'adda tare da mayaƙansa guda biyar yayin wani artabu a ƙaramar hukumar Igabi ta jihar
  • Jami'an tsaron bayan sun samu nasarar sheƙe ƴan ta'addan, sun ƙwato makamai masu tarin yawa da wasu kayayyaki a hannunsu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Dakarun rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) sun samu nasarar hallaka wani shugaban ƴan ta'adda a jihar Kaduna.

Sojojin sun hallaka shugaban ƴan ta'addan ne mai suna Mustapha Abdullahi tare da wasu mayaƙa guda biyar a ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda a Kaduna
Dakarun sojojin sama sun hallaka shugaban 'yan ta'adda Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Kakakin rundunar NAF, AVM Edward Gabkwet ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

A karo na 2, ƴan sanda sun gayyaci shugaban NLC kan sabon zargi, ɓayanai sun fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda sojoji suka hallaka ƴan ta'adda

AVM Edward Gabkwet ya ce an kai farmakin ne a ranar 31 ga watan Agustan 2024, biyo bayan rahoton sirri da aka samu cewa an ga ɗan ta’addan tare da ƴan ƙungiyarsa biyar a kusa da dajin Sabon Gida da ke kan titin Sabon Birni a ƙaramar hukumar Igabi.

Kakakin ya ce bayanan sirri sun kuma nuna cewa akwai yiwuwar ƴan ta’addan na shirin yin garkuwa da fararen hula wanda hakan ya sanya aka tura tawagar rundunar ta musamman zuwa wurin, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.

"Bayan ƴan ta'addan da ke kan babura sun hango jami’an tsaron na musamman, nan take sai suka buɗe wuta, inda sojojin suka yi mayar da martani tare da samun nasarar hallaka ƴan ta’addan."

- AVM Edward Gabkwet

AVM Ya bayyana cewa, sojojin sun ƙwato bindigogi ƙirar gida guda biyar, ƙananan bindigogi ƙirar gida, harsasai, laya iri-iri da layukan waya daga hannun ƴan ta’addan.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kashe ƴan bindiga sama da 1,000, sun ceto ɗaruruwan mutane a Najeriya

Sojoji sun hallaka ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin saman Najeriya ta bayyana cewa dakarunta sun kai hare-hare kan ƴan ta'aɗɗa a jihar Borno.

Rundunar sojojin saman ta ce hare-haren da aka kai a yankin Tumbun da ke kusa da tafkin Chadi, sun yi sanadiyyyar hallaka ƴan ta'adda masu yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng