Gina Gidaje 500 A Kano: Dan Kwangila Ya Harzuka Minista, an Gindaya Masa Sharuda

Gina Gidaje 500 A Kano: Dan Kwangila Ya Harzuka Minista, an Gindaya Masa Sharuda

  • Ministan ma'aikatar gidaje da raya birane, Ahmed Musa Dangiwa ya ziyarci inda gwamnati ke gina gidaje 500 a karamar hukumar Tofa ta Kano
  • Rukunin gidajen wanda aka yiwa lakabi da 'Renewed Hope' na daga cikin shirin gwamnatin Bola Tinubu na wadatar da 'yan Najeriya da muhalli
  • A yayin ziyarar ne, ministan ya gano irin tafiyar hawainiyar da aikin ke yi inda ya gargadi dan kwangilar akan ya tashi tsaye ko ya rasa aikin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Ma’aikatar gidaje da raya birane ta tarayya ta fara aikin gina gidaje 500 a jihar Kano kamar yadda gwamantin Bola Tinubu ta yi alkawari.

An ce za a gina gidajen 500 a tsari uku: Gida mai dakuna 2, gida mai daki 1, da kuma gida mai dakuna 3 wanda ake sa ran marasa karfi ne za su samu.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya dauko kammala aikin Kwankwaso, ya yiwa dan kwangila barazana

Gwamnatin tarayya ta fara gina gidaje 500 a jihar Kano
Ministan Tinubu ya fusata da dan kwangilar da ke gina gidaje 500 a jihar Kano. Hoto: @fmhud_ng
Asali: Twitter

Dan kwangila ya fusata minista

Rukunin gidajen wanda aka yiwa lakabi da 'Renewed Hope', ana gina shi ne a kauyen Lambu da ke karamar hukumar Tofa ta jihar Kano, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da ya ke jawabi, ministan ma'aikatar, Ahmed Musa Dangiwa ya nuna bacin ransa kan yadda dan kwangilar da aka ba aikin gina gidajen ya ke yiwa aikin rikon sakainar kashi.

Arc. Ahmed Dangiwa ya gargadi dan kwangilar da ya tashi tsaye ya kammala aikin a kan lokaci ko kuma ya fuskanci barazanar kwace wannan kwangilar.

Minista ya gargadi dan kwangila

Ministan ma'aikatar ta gidaje da raya birane ya shaidawa dan kwangilar cewa:

"Ba mu gamsu da yadda ake gudanar da aiki a nan ba. Mun yi tunanin za mu zo mu taras da cewa aikin ku ya yi nisa sosai, amma sai muka ga akasin hakan.

Kara karanta wannan

Yayin da ambaliya ke rusa gidajen Kaduna, gwamnatin Uba Sani za ta gina sabon birni

"Ya zama wajibi ka kara azama, domin idan muka dawo mako mai zuwa ba mu tarar da wani ci gaba ba, to za mu kwace wadanda ba ka gama ba mu ba wani dan kwangilar ya karasa.

Gina gidajen 'Renewed Hope'

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta bullo da shirin samar da gidaje na Renewed Hope domin shwo kan matsalar karancin gidaje a kasar nan.

Mutane masu kanana da matsakaitan samun kudi ne za su iya mallakar gidajen ta hanyar 'biya daya, zabin jinginar da kadara, ko kuma ta hanyar zaman haya zuwa mallaka.'

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.