Zamfara: Gwamnati Ta ba da Tallafin Kudi da Filaye ga Wadanda Ambaliya Ta Shafa

Zamfara: Gwamnati Ta ba da Tallafin Kudi da Filaye ga Wadanda Ambaliya Ta Shafa

  • Gwamnatin jihar Zamfara ta kai dauki ga mutanen da ambaliyar ruwa ta ritsa da su a karamar hukumar Gummi da ke jihar
  • Gwamnan jihar, Dauda Lawal ya sanar da ba da tallafin Naira miliyan 100 ga wadanda abin ya shafa tare da kuma ba su tallafin kayan abinci
  • Gwamnatin ta kuma sanar da cewa ta ware filaye ga wadanda suka rasa muhallansu domin su gina sababbin gidaje nesa da garuruwansu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da tallafin Naira miliyan 100 ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a karamar hukumar Gummi da ke jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a lokacin da ya kai ziyarar tantance irin barnar da ambaliyar ta yi a karamar hukumar da abin ya shafa.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan ambaliyar ruwa ta lalata gidaje sama da 10,000 a jihar Arewa

Gwamnan Zamfara ya kai dauki ga wadanda ambaliya ta ritsa da su a jihar
Zamfara: Gwamnati ta raba kudi da filaye da mutanen da ambaliya ta ritsa da su. Hoto: @daudalawal
Asali: Facebook

Gwamna ya ba jama'a tallafi

Da ya ke jajanta wa mutanen, ya kuma bayar da umarnin a raba musu buhuna 10,000 na nau'ikan hatsi daban daban, tare da gidajen sauro da barguna, inji rahoton Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“A yau, na zo karamar hukumar Gummi domin yin ta’aziyya tare da gudanar da bincike kan al’ummomin da ambaliyar ruwa ta shafa a makon jiya.
“Ina so sanar da ku cewa na bayar da gudunmawar buhunan abinci guda 10,000 da suka hada da shinkafa, masara, da gero, domin raba wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa.

Gwamna ya ba da matsugunni

Baya ga kayan abinci, FRCN ta ruwaito Gwamna Dauda ya ce akwai tallafin kudi da kuma samar da matsugunni, inda ya ke cewa:

“Haka zalika, a madadin gwamnatin jihar Zamfara, ina sanar da ku cewa za mu tallafa wa wadanda ambaliyar ta shafa da Naira miliyan 100.

Kara karanta wannan

Gobara ta babbake rukunin gidajen ma'aikatan gwamnati, bayanai sun fito

Bugu da kari, duk wadanda abin ya shafa, za a raba musu filaye nesa da yankin da ke da hadarin ambaliyar domin su gina sababbin gidaje.”

Gwamna Lawal ya kuma yi alkawarin magance matsalar ambaliyar ruwa ta hanyar gina sababbin magudanan ruwa, gyaran madatsun ruwa, da duba yiwuwar gina wasu sababbi.

Matawalle ya ba da tallafin N20m

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon gwam nan jihar Zamfara kuma karamin ministan tsaro, Bello Mawatalle ya ba da tallafin N20m ga mutanen da ambaliya ta ritsa da su a Zamfara.

An ce Bello Matawalle, wanda ya ba da tallafin ne ga 'yan karamar hukumar Gummi da ambaliya ta mamaye muhallansu da gonakinsu sakamakon mamakon ruwan sama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.