Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje 110 a Zamfara

Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje 110 a Zamfara

Akalla gidaje 110 sun zagwanye a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara, biyo bayan wata musiba ta ambaliyar ruwa da ta auku a ranar Laraba.

Hakan yana kunshe cikin sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar a ranar Juma’a cikin Gusau, babban birnin jihar kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta wallafa.

Sanarwar ta fito ne daga bakin mai ba Gwamna Bello Matawalle shawarwari na musamman kan harkokin jin kai, kula da bala’o’i da ci gaban al’umma, Fa’ika Ahmad.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa, Zurmi tana daya daga cikin kananan hukumomi bakwai da hukumar kula da yanayi NIMET ta yi hasashen za su fuskanci ambaliyar ruwa a daminar bana.

Ambaliyar ruwa
Ambaliyar ruwa
Asali: UGC

A sanarwar da Hajiya Fa’ika ta fitar, ta bayyana farin cikin yadda babu asarar rai ko daya da aka samu yayin da ambaliyar ruwan ta auku, sai dai ta bayyana damuwa kan asarar muhallai da ta janyo wa dubban mutane.

Dalilin haka ya sanya kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara, Nasiri Magarya, a ranar Alhamis ya jagoranci tawaga domin kai ziyarar jaje ga mutanen da musibar ta auku kansu a garin Zurmi.

Ya gabatar musu da kayayyakin tallafi da gwamnatin jihar ta ba da gudunmuwa.

A wani rahoto da Legit.ng ta ruwaito, Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa NEMA, ta ce za'a yi ambaliyar ruwan sama a kananan hukumomi 102 na jihohi 28 da ke fadin tarayya a bana.

Darekta Janar na hukumar, Muhammad Muhammad, shi ne ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar ranar Juma'a, 10 ga watan Yuli, 2020.

Darektan ya ce an yi hasashen hakan ne sakamakon rahoton da ma'aikatar lura da al'amuran ruwa a Najeriya (NIHSA) ta saki.

KARANTA KUMA: Jami'ar KUST Wudil ta daga likafar malamai 17 zuwa furofesoshi

Muhammad Muhammad ya ce karamar hukumar Kaura da Zariya a jihar Kaduna na cikin wadanda ke cikin mummunan hadarin ambaliya.

Ya ce hukumomin agaji su wayar da kan al'umma a kan su kasance cikin shirin yin hijira daga muhallansu.

Hakazalika ya shawarci gwamnatoci su kasance a cikin shirin yadda za su dakile aukuwar wannan musiba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng