Matawalle Ya Fadi Shirin Kawo Karshen Bello Turji da Sauran Manyan 'Yan Bindiga
- Ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle zai jagoranci gagarumin shirin kawo ƙarshen ƴan bindigan da suka addabi yankin Arewa maso Yamma
- Matawalle ya umarci babban hafsan tsaro na ƙasa da sauran hafsoshin tsaro su koma Sokoto domin kawo ƙarshen ƴan bindiga
- Ministan wanda shi ma zai kasance a Sokoto, ya sha alwashin kawo ƙarshen ƴan bindigan da suka addabi mutanen yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya sanar da wani gagarumin shiri na yaƙi da ƴan bindiga.
Shirin na ƙoƙarin kawo ƙarshen ƴan bindigan za a yi shi ne kan miyagun da suka addabi jihohin Sokoto, Zamfara, Katsina, da Kebbi.
Daraktan yaɗa labarai na ma’aikatar tsaro, Henshaw Ogugbike ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matawalle ya koka kan rashin tsaro
Matawalle ya nuna matuƙar damuwarsa kan rashin tsaron da ake fama da shi a yankin Arewa maso Yamma, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.
Ya bayyana cewa an umurci babban hafsan tsaron ƙasa da sauran manyan hafsoshin soji da su haɗu da shi a Sokoto, inda nan ne hedkwatar rundunar da ke yaƙi da ƴan bindiga a yankin.
Wane alwashi ministan ya sha kan Bello Turji?
Ministan ya sha alwashin cewa gwamnatin tarayya za ta yi amfani da duk abin da ya dace domin fatattakar shugaban ƴan bindiga nan Bello Turji da tawagar mayaƙansa.
"Ba za mu ƙyale waɗannan ƴan bindigan da ƴan ta’adda su ci gaba da muzgunawa mutanenmu ba."
"Lokacinsu ya zo ƙarshe. Za mu raunana sansanonin su, mu maido da zaman lafiya a cikin al’ummominmu."
- Bello Matawalle
Matawalle wanda zai kasance tare da hafsoshin tsaron, ya tabbatarwa al’ummar Sokoto, Zamfara, Katsina, da Kebbi cewa, rundunar sojoji ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba a ƙoƙarin kawar da ƴan bindiga daga yankin.
Ya kamata a kawo ƙarshen ƴan bindiga
Muhammad Auwal ya shaidawa Legit Hausa cewa tun tuni ya kamata a ce gwamnati ta tashi tsaye ta kawo ƙarshen ƴan bindiga.
Ya bayyana cewa matakin da gwamnatin ta ɗauka zai nuna cewa da gaske take yi wajen kawo ƙarshen matsalar rashin tsaron.
"Idan da gaske suke yi za su koma can su tare, ina ganin ba za a daɗe ba za a kawo ƙarshen miyagun nan. Ƴan ta'addan an san inda suke, kamata ya yi a je a rufar musu kawai."
- Muhammad Auwal
Matawalle ya fusata kan kisan Sarkin Gobir
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle ya yi Allah wadai da kisan hakimin Gatawa dake ƙaramar hukumar Sabon Birni a Sakkwato wanda aka fi sani da Sarkin Gobir.
Matawalle ya bayyana kisan sarkin Gobir, Muhammad Isa Bawa a matsayin ɗanyen aiki na rashin imani, inda ya ce duk mai hannu a kisan zai ɗanɗana kuɗarsa.
Asali: Legit.ng