Gwamnati Ta Na Zargin Mutuwar Kwamishinan Yan Sanda, Ta Kafa Kwamiti

Gwamnati Ta Na Zargin Mutuwar Kwamishinan Yan Sanda, Ta Kafa Kwamiti

  • Gwamnatin jihar Lagos ta kafa kwamiti na musamman domin binciken sanadin mutuwar kwamishinan yan sanda a Akwa Ibom
  • An sanar da mutuwar Waheed Ayilara a jihar Lagos a ranar Alhamis 29 ga watan Agustan 2024 bayan yi masa tiyata a asibiti
  • Kwamishinan lafiya a jihar, Akin Abayomi shi ya ba da umarnin a madadin gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu domin fara bincike

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Bisa ga dukan alamu gwamnatin jihar Lagos tana kokwanton mutuwar kwamishinan yan sanda na jihar Akwa Ibom.

Gwamnatin jihar ta kafa kwamitin lafiya domin bincike kan musabbabin mutuwar Wahedd Ayilara bayan yi masa tiyata.

Gwamnati ta fara binciken mutuwar kwamishinan 'yan sanda
Gwamnatin jihar Lagos ta kafa kwamiti domin binciken mutuwar kwamishinan 'yan sanda, Waheed Ayilara. Hoto: @officerTimzy.
Asali: Twitter

An fara binciken mutuwar kwamishinan 'yan sanda

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya dauko kammala aikin Kwankwaso, ya yiwa dan kwangila barazana

Kwamishinan lafiya a jihar, Akin Abayomi shi ya umarci fara binciken a yau Asabar 31 ga watan Agustan 224, cewar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abayomi ya ba da umarnin ne a madadin gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu domin zurfafa bincike kan lamarin, Punch ta tattaro.

Gwamnatin ta kuma jajantawa iyalan marigayin da al'umma kan wannan babban rashi da aka yi inda ta ce tabbas Ayilara mutumin kirki ne.

Lagos: Musabbabin binciken mutuwar kwamishinan 'yan sanda

"Duba da yadda marigayin ya mutu jim kadan bayan kammala tiyata, ma'aikatar lafiya ta samu umarni daga gwamna domin kafa kwamitin lafiya saboda binciken dalilin mutuwarsa."
"Wannan kwamitin zai samu jagorancin daraktan asibitin koyarwa na LASUTH, Farfesa Adetokunbo Fabanwo inda zai gabatar da rahoto cikin kwanaki bakwai."
"Muna jajantawa tare da ba da hakuri kan abin da wannan umarni zai jawo, muna tabbatarwa al'umma cewa gwamnatin Lagos ta himmatu wurin yin kwakkwaran bincike."

Kara karanta wannan

Gwamna a Arewa ya shirya zaben ciyamomi, ya ayyana Juma'a a matsayin ranar hutu

- Akin Abayomi

Kwamishinan 'yan sandan Akwa Ibom ya rasu

A wani labarin, kun ji cewa An shiga alhini matuka bayan sanar da rasuwar Kwamishinan yan sanda a jihar Akwa Ibom.

Marigayi Waheed Ayilara ya rasu da safiyar ranar Alhamis 29 ga watan Agustan 2024 a asibitin koyarwa na Jami'ar Lagos.

Kafin rasuwarsa, Ayilara ya rike muƙamin mukaddashin kwamishinan yan sanda a jihar Lagos wanda aka naɗa shi a watan Nuwambar 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.