Ana Zargin Abubuwa 2 Suka Tilasta Murabus din Shugaban Hukumomin DSS da NIA

Ana Zargin Abubuwa 2 Suka Tilasta Murabus din Shugaban Hukumomin DSS da NIA

  • Ana ta zargin Bola Tinubu ya bukaci shugabannin DSS da NIA su yi murabus saboda rashin kwarewa a ɓangarensu
  • Rahotanni sun bayyana cewa ran Tinubu da Nuhu Ribadu ya ɓaci kan rashin kawo bayanai game da zanga-zanga da kwace jiragen Najeriya
  • Wannan na zuwa ne bayan murabus din Yusuf Magaji Bichi na hukumar tsaro ta DSS da kuma Abubakar Ahmed na NIA

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Rahotanni da muke samu sun bayyana dalilin da ya sa Bola Tinubu ya bukaci shugabannin DSS da NIA su yi murabus.

Bayanan suka ce an bukace su ne saboda kwace jiragen saman Najeriya da kuma zanga-zanga da aka gudanar a kasar a ranar 1 ga watan Agustan 2024.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta yi magana kan zargin shirin korar Ganduje daga mukaminsa

Ana zargin rashin kwarewa ya tilasta shugabannin DSS da NIA murabus
Rahotanni sun fadi 'dalilin' murabus din shugabannin DSS da NIA. Hoto: @abba_yusufbichi, @officialABAT.
Asali: Twitter

An zargi dalilin Bichi na yin murabus

Rahoton Punch ya ce Tinubu da Nuhu Ribadu sun yi korafi kan rashin samun bayanai daga hukumomin kan matsalolin guda biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan ba ku mantaba, Yusuf Bichi ya yi murabus daga shugabancin DSS yayin da Ahmed Abubakar ya bar muƙamin shugaban NIA.

Majiyoyin sun tabbatar da cewa ana zargin Bichi da rashin kawo bayanai game da zanga-zanga da aka yi a kasar.

Sai kuma Abubakar na hukumar NIA kan rashin samun bayanai kafin kwace jiragen saman Najeriya guda uku.

Ran Tinubu, Ribadu ya ɓaci kan hukumomin

An tabbatar da cewa abubuwan guda biyu sun batawa Tinubu da Ribadu rai wanda suke ganin abin kunya ne ga Najeriya.

Har ila yau, sun nuna rashin gamsuwa kan kokarin shugabannin hukumomin guda biyu a kasar da ya rage mata kima a idon duniya.

Kara karanta wannan

Ajuri Ngelale, Lalong da sauran mutum 5 da suka ajiye mukamai a gwamnatin Tinubu

DSS: An fayyace bidiyon da ake yadawa

A wani labarin kun ji cewa tsohon daraktan hukumar DSS, Mike Ejiofor ya yi magana kan bidiyon da ake yadawa a kafafen sadarwa.

Ejiofor ya ce bidiyon da ake yadawa cewa ma'ikatan DSS na murnar korar Yusuf Bichi tsohon zance ne wanda aka dauka tun 2018.

Ejiofor ya ce ya kamata sabon babban daraktan hukumar, Adeola Ajayi ya fayyacewa al'umma matsayin bidiyon da ake yadawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.