Mai Karfi Sai Allah Ya Isa: Yadda Aka Daure Matashi a Magarkama Kan Tura Sakon Ajiye Aiki Ta Waya
- Wani matashi ya shiga firgici bayan da aka kama shi tare da garkame shi a kotu da sunan ya aikata laifin sata da zagin mai gidansa
- A hirar da aka yi dashi, ya ce an garkame shi ne saboda kawai ya nuna rashin jin dadinsa da yadda yake aiki a kamfanin mai gidansa
- Sai dai, rahoto da zargin da ake ya nuna cewa, ana zargin ya saci waya ne tare da tura sako mai tunzura mutum ga mai gidansa
FCT, Abuja - Wani matashin mai daukar hoto, Peter Nicholas ya shafe watanni 10 a gidan gyaran hali na Keffi bayan da ya tura sakon ajiye aiki ga uban gidansa ta wayar salulu.
Wannan lamari ya faru ne a birnin Abuja, inda matashin ya bayyana cewa, ya samu aiki ne da kamfanin daukar hoto na wani attajiri a babban birnin tarayya.
Da yake bayyana yadda ya fara aikin, ya ce an dauke shi aiki ba tare da wata takarda ba, kuma ganin yadda aka wulakanta wasu abokan aikinsa ne ya cire masa kaunar aiki da attajirin.
Yadda ya tura sakon barin aiki
Sai dai, a cewarsa, yayin da ya tura sakon barin aikin a ranar 10 ga watan Oktoban 2023, mai gidan nasa bai amsa ba, kamar yadda ya shaidawa Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka nan, ya kuma sake tura sakon ajiye aikin ta wayar salulu tare da ba mai gidan nasa shawarin koyon zamantakewa da iya ji da ma’aikatansa a ranar 14 ga watan Oktoban.
A ranar 15 ga watan Oktoba ne aka damke shi tare da gurfanar dashi a gaban Kotun Yanki da ke Mpappe a a Abuja.
An zarge shi da zagin mai gidansa da kuma tafka sata
A tattaunawarsa da jaridar Punch, ya bayyana yadda aka tuhume shi da laifuka, inda ya karyata hakan a gaban kotu.
Daga cikin laifukan da aka zarge shi da aikatawa, an ce ya saci wayar salulu, wanda yace sam ba haka bane.
Hakalika, ya ce bai amsa laifin bata sunan mai gidan nasa ba, duk da amsa cewa ya tura sakon ta wayar salula.
Yadda aka fitar dashi daga magarkama
Da yake amsa tambaya kan yadda ya shafe lokaci da kuma yadda aka fitar dashi, ya ce wani abokinsa ne ya kai batun gaban wata kungiya mai zaman kanta, Hope Behind Bars Afrika, inda aka gaggauta kawo masa dauki.
Matasan Najeriya da dama kan shiga magarkama ba tare da wani laifi ba, wanda ke taba rayuwarsu da kuma lafiyar tunaninsu.
Haka dai Peter ya bayyana yadda ya shiga damuwa tare da shafe watanni 10 ba tare da aikata wani laifin a zo a gani ba.
Batun zaman Bobrisky a magarkama
A wani labarin, bayanan da suke fitowa sun bayyana cewa hukumar kula gidajen gyaran hali ta Najeriya (NCS) ta mayar da Idris Okuneye wanda aka fi sani da Bobrisky Kirikiri daga Ikoyi.
An yanke wa Bobrisky hukuncin daurin watanni shida a gidan gyaran hali ne bisa laifin cin zarafin Naira.
Jaridar Leadership ta tabbatar da cewa sabon rahoton ya sabawa rahotannin da ke cewa ana tsare da Bobrisky ne a gidan gyaran hali na Ikoyi.
Asali: Legit.ng