Gwamna Abba Ya Dauko Kammala Aikin Kwankwaso, Ya Yiwa Dan Kwangila Barazana

Gwamna Abba Ya Dauko Kammala Aikin Kwankwaso, Ya Yiwa Dan Kwangila Barazana

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dauko aikin kammala titin da ke Kunci a karamar hukumar Ghari
  • An bayar da kwangilar fara titin a lokacin mulkin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso na biyu
  • Gwamnatin Kano ta yi barazanar kwace aikin daga dan kwangila da aka ba aikin titin tun da fari idan ya gaza

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da aikin titin garin Kunci da ke karamar hukumar Ghari a Kano.

An fara aikin titin mai tsawon kilomita biyar tun a zamanin mulkin Rabi'u Musa Kwankwaso na biyu a jihar.

Kara karanta wannan

Yayin da ambaliya ke rusa gidajen Kaduna, gwamnatin Uba Sani za ta gina sabon birni

Gwamna
Gwamnatin Kano za ta kammala aikin titin da Kwankwaso ya fara Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa a sanarwar da darakta janar kan yada labaran gwamna, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, an zargi gwamnatin Ganduje da watsi da aiki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Abba ya yaba da hakurin mazauna yankin, inda ya ce gwamnati na tare da su domin ci gaba da samar da ayyukan inganta rayuwarsu.

Gwamna Abba ya gargadi dan kwangila

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya gargadi dan kwangilar da gwamnatin Kwankwaso ta ba kwangilar titin gari ya gaggauta dawowa aiki.

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta kwace kwangilar daga hannun kamfanin matukar bai dawo ci gaba da aikin da aka yi yaryajeniya zai yi ba.

The Guardian ta wallafa cewa gwamnan ya ba kamfanin wa'adin mako guda ya gaggauta kawo kayan aikinsa domin ci gaba da ginin hanyar.

Kara karanta wannan

TSA: Abba ya sa a rufe dukkanin asusun bankin hukumomi da ma’aikatun Kano

Abba: Gwamnan Kano ya kaddamar da aiki

Kafin kaddamar da aikin titin garin Kunci, gwamna Abba Kabir Yusuf da tawagarsa sun kaddamar da wani aikin.

Gwamnan ya bude aikin titin garin Yandadi, sannan sun ziyarci kwalejin ilimi ta Ghari inda ya yi alkawarin cigaba da ayyukan raya kasa.

Gwamna Abba ya fara aikin titin

A wani labarin kun ji cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya fara kokarin kammala titin Dorayi wanda gwamnatin tarayya ta fara a zamanin Muhammadu Buhari.

Gwamna Abba ya bayyana cewa ya sa sane da yadda mazauna Dorayi zuwa Panshekara suka dade suna rokon a kammala aikin titin, shi ya sa za a yi masu shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.