Mahaifiyar Zainab Bayero Ta Fadi Silar Shigansu Wannan Hali, Ta Roki Tinubu, Shettima

Mahaifiyar Zainab Bayero Ta Fadi Silar Shigansu Wannan Hali, Ta Roki Tinubu, Shettima

  • Yayin da ake sukar Zainab Ado Bayero, mahaifiyarta ta yi magana kan halin da suke ciki da gwagwarmayar da suka yi a baya
  • Hauwa Momoh wacce yar marigayi Otaru na Auchi ne ta ce tun bayan mutuwar Ado Bayero suka fada matsala
  • Ta bayyana yadda ta zo Kano har suka hadu da basaraken duk da nuna mata wariya da aka yi a wancan lokacin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Mahaifiyar Zainab Ado Bayero ta yi magana kan caccakar yarta da ake yi a kafofin sadarwa.

Hauwa Momoh ta ce ba za ta iya cigaba da ganin yadda ake sukar yarta ta ba kan maganganun da ta yi.

Kara karanta wannan

'Bello Turji ya zama hafsun sojoji?' Dalung ya yi zazzafan martani ga gwamnatin Tinubu

Mahaifiyar Zainab Ado Bayero ta yi karin haske kan halin da suke ciki
Mahaifiyar Zainab Bayero, ta fadi halin da suke ciki bayan rasuwar Ado Bayero. Hoto: Zainab Jummai Ado Bayero.
Asali: Facebook

Mahaifiyar Zainab Bayero ta koka da rayuwa

Vanguard ta tattaro cewa Momoh ya yanke shawarar fadan abin da ke faruwa da su da halin da suke ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta nuna damuwa kan halayyar mutane game da Zainab inda ta ce babu uwar da za ta so ana yakar yarta haka.

"Sunana Princess Hauwa Momoh, ni yar marigayi Otaru na Auchi, Alhaji Guruza Momoh ne, na ji zafin abin da ake yiwa yata, Zainab mutum ce mai kunya kuma mai natsuwa."
"Tun ina shekaru 18 na so karanta aikin jarida a BUK, amma mahaifiyarta ta ce ya yi nisa, amma mahiaifina ya rubuta wasika ga marigayi Ado Bayero domin kula da ni."
"Ban taba tsammanin zuwa Kano zai sauyamin rayuwa ba, marigayi ya nuna yana sona inda aka nunamin kiyayya saboda ba daga Arewa na ke ba, amma ya matsa a kan yana sona."

Kara karanta wannan

Magani na gagarar talaka: Masu ciwon sukari sun nemi alfarma wajen Shugaba Tinubu

"Haka na amince, duk da kasancewa ta yar sarauta kuma Musulma amma na cigaba da fuskantar wariya, ita ma Zainab ta fuskanci haka musamman lokacin da ta ke Firamare a Kano."

- Hauwa Momoh

Hauwa Momoh ta roki Tinubu, Shettima

Dattijuwar ta ce bayan rasuwar basaraken ne suka sake fuskantar wariya na musamman har aka hana su gadonsu.

Daga karshe ta bukaci taimako daga Bola Tinubu da mataimakinsa da sauran al'umma su taimaka musu domin cire su a wannan kangi.

Zainab ta sake neman taimako

Kun ji cewa diyar marigayi Ado Bayero ta sake rokon Gwamna Abba Kabir na jihar Kano taimako na musamman.

Zainab Ado Bayero ta ce taimakon da gwamnan ya yi musu a baya bai ishe su inda ta gode masa kan kokarinsa.

Diyar marigayin ta bayyana irin halin da suka tsinci kansu a ciki bayan rasuwar marigayi inda ta ce suna bukatar wurin zama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.