Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya 3 da ba Su da Ministoci a Mulkin Bola Tinubu
Abuja - Watanni kadan da zama shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya zabi wadanda yake so su zama ministocin tarayya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sai dai a halin yanzu jihar Filato ba ta da wakilci a majalisar zartarwa (FEC) a sakamakon murabus da Sanata Simon Lalong ya yi.
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Babu wasu Ministoci a gwamnatin tarayya
Bayan Simon Lalong da ya zama Sanata an kuma dakatar da Betta Edu daga aiki saboda zargin rashin gaskiya a ma'aikatar jin-kai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ganin an yi watanni takwas, Daily Trust ta rahoto cewa mutanen Filato sun fara kokawa, suna rokon shugaban kasa ya tuna da su.
Rahoton nan ya tattaro jerin ma’aikatun da ba su da manyan ministoci a sakamakon sauyin da aka samu a majalisar zartarwa (FEC).
1. Ma’aikatar jin kai da yaki da talauci
Dakatar da Betta Edu domin a gudanar da bincike a ma’aikatar jin kai da yaki da talauci ya sa aka shafe watanni takwas babu minista.
Har zuwa yanzu babu labarin nadin ministan rikon kwarya, duk da Edu ba ta ofis, jihar Kuros Ribas ta na da wakilci a majalisar FEC.
2. Ma’aikatar kwadago da samar da ayyuka
Tun a karshen 2023, babu babban Minista a ma’aikatar kwadago da samar da ayyuka a sakamakon murabus da Simon Lalong ya yi.
Shugaban kasa bai karawa Nkiruka Onyejeocha matsayi ba wanda har yanzu ita ce karamar minister a gwamnatin Bola Tinubu.
3. Ma’aikatar bunkasa kiwon dabbobi
Shugaba Bola Tinubu ya kirkiro ma’aikata ta musamman domin bunkasa kiwon dabbobi a Najeriya amma ba a nada minista ba tukuna.
Kafin nan an nada Attahiru Jega ya ja ragamar kwamitin da zai yi wannan aiki, zuwa yanzu an zura idanu domin ganin ministan farko.
Jami'an gwamnatin tarayya da suka yi murabus
Akwai manyan jami’an da suka ajiye mukaminsu, suka bar aiki a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu kamar yadda rahoto ya gabata a baya.
Wanda ya fara bin wannan layi lokacin da aka canza gwamnati shi ne tsohon shugaban hukumar NUC, Farfesa Abubakar Rasheed.
Asali: Legit.ng