Sunayen Shugabannin Hukumar NIA daga Kafuwarta a 1986 Zuwa 2024
Abuja - A tsakiyar shekarar 1986, shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida ya dadatsa hukumar tsaro na kasa watau NSO.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Wannan aiki da Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya yi ya haifar da hukumomin NI masu fararen kaya da DIA da NIA masu leken asiri.
Rahoton nan ya jero sunayen shugabannin da suka jagoranci NIA daga lokacin zuwa yau.
Shugabannin hukumar NIA a tarihi
1. Cif Albert K. Horsfall
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Cif Albert K. Horsfall ya fara shugabantar hukumar NOA daga lokacin da aka kafa ta a shekarar 1986 daga baya kuma ya rike DSS.
2. Haliru Akilu
Birgediya Janar Haliru Akilu da aka fi sani da Ali Akilu ya zama shugaban hukumar tsakanin 1990 har zuwa shekarar 1993
3. Ambasada Zakari Y. Ibrahim
Ambasada Zakari Y. Ibrahim ya dade a ofis, shi ya jagoranci NIA na tsawon shekaru kimanin biyar daga 1993 har zuwa 1998.
4. Ambasada Godfrey B. Preware
Shi kuwa Ambasada Godfrey B. Preware daga Bayelsa bai dade yana rike da NIA ba, ya yi watanni ne daga 1998 zuwa Yunin 1999.
5. Ambasada Uche O. Okeke
Olusegun Obasanjo ya nada Uche O. Okekeya zama shugaban hukumar leken asirin, ya yi shekaru bakwai sai ya sauka a 2007.
6. Ambasada Emmanuel E. Imohe
Daga 2007, Ambasada Emmanuel E. Imohe ya jagoranci NIA zuwa Satumban 2009. Imohe ya taba zama shugaban yarjejeniyar ATT.
7. Ambasada Olaniyi Oladeji
Bayan Imohe sai aka dauko Amb. Olaniyi Oladeji wanda ya shafe shekaru hudu da wasu ‘yan kwanaki a matsayin shugaban NIA ta kasa.
8. Ambasada Ayo Oke
A ‘yan kwanakin nan Ayo Oke yana cikin shugannin NIA da aka fi sani saboda badakalar da ta faru a lokacinsa, a 2017 ne aka tsige shi.
9. Ahmed Rufai Abubakar
Shekaru shida Ahmed Rufai Abubakar ya yi a ofis a matsayin shugaban NIA. Muhammadu Buhari ya nada shi a 2018 sai ya sauka a 2024.
10. Muhammad Muhammad ya zama shugaban NIA
Bayan shekaru kusan bakwai, Ahmad Rufai Abubakar ya tattara ya bar kujerarsa ta Darekta Janar na NIA, sai aka nada Muhammad Muhammad.
Shugabannin hukumar DSS a tarihi
Ku na da labari cewa shugaban farko da aka yi a tarihin DSS shi ne Ismail Gwarzo da Ibrahim Babangida ya nada a shekarar 1986.
Muhammadu Buhari ya maido Lawal Daura aiki kafin Yemi Osinbajo ya fatattake shi a 2018 da DSS ta aukawa shugabannin majalisa.
Asali: Legit.ng