“Ka Ji Tsoron Allah”: Sheikh Dutsen Tanshi Ya Soki Tsohon Minista, Farfesa Pantami
- Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Abdulaziz Idris Dutsen Tanshi ya dira kan tsohon Minista, Farfesa Isa Ali Pantami
- Shehin malamin ya koka kan yawan fadan maganganu da ba gaskiya ba da tsohon Ministan ke yawan yi a mafi yawan lokuta
- Malamin ya caccaki tsohon Ministan bayan ya ce ya san yadda za a yi marigayi Sarkin Gobir ya fito bayan kama shi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Bauchi - Sheikh Abdulaziz Idris Dutsen Tanshi ya caccaki tsohon Minista, Farfesa Isa Ali Pantami.
Malamin yana magan ne bayan Ministan a baya ya umarci hada layuka da lambar NIN saboda yaki da 'yan ta'adda.
Sheikh Dutsen Tanshi ya ci gyaran Farfesa Pantami
An ji Shehin malamin ya bayyana haka a faifan bidiyo yayin hudubar Juma'a da ya wallafa a Facebook a jiya Juma'a 30 ga watan Agustan 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sheikh Dutsen Tanshi ya ce mafi yawan maganganun tsohon Ministan akwai rashin gaskiya a ciki saboda mafi yawansu sai ya kauce hanya.
Sheikh Idris ya shawarci Isa Pantami
"Lokacin da kake Minsita ka wahalar da mutane suna kwana layi kan hada layuka da lambar NIN sai yanzu ne za ka ce ka san yadda Sarkin Gobir zai fito."
"Sai yanzu ne ka san da haka, wallahi idan nine kai ba zan sake magana kan haka ba, wannan ai rashin kunya ne, lokacin kana kan mukamin ba ka dakile layukan 'yan ta'adda ba."
- Sheikh Abdulaziz Idris Dutsen Tanshi
Sarkin Gobir: Pantami ya jajanta kan lamarin
Kun ji cewa Tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Ali Isa Pantami ya yi Allah wadai da kisan gillar da yan ta'adda su ka yiwa Sarkin Gobir, Alhaji Isa Bawa.
A sakon da ya wallafa a shafins Facebook, Isa Pantami ya yi addu'ar Allah ya yi wa marigayin rahama, tare da dukkanin wadanda su ka rasu a hannun miyagun.
Farfesa Isa Ali Pantami ya yi tir da kisan Sarkin Gobir, Alhaji Isa Bawa duk da neman daukin gwamnati da ta sauran masu ruwa da tsaki.
Asali: Legit.ng