"Muna kan Aiki," Gwamna Ya Faɗi Matakin da Ya Ɗauka kan Biyan Sabon Albashin N70,000
- Gwamna Agbu Kefas ya ce tuni gwamnatinsa ta fara shirin biyan ma'aikata sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000
- Kefas ya sanar da hakan ne a gidan gwamnatinsa da ke Jalingo jim kaɗan bayan rattaɓa hannu kan dokar ƙarin kasafin kuɗin 2024
- Gwamnan ya ce zai yi kokari daidai gwargwado wajen cikawa talakawan jihar Taraba murdansu ta hanyar sauke nauyin da suka dora masa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Taraba - Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas ya bayyana cewa tuni gwamnatinsa ta fara aiki kan yadda za a aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi.
Gwamna Kefas ya ce ya ɗora alhakin lamarin kan ofishin shugaban ma'aikatan jihar kuma tuni aiki ya yi nisa don fitar da tsarin aiwatar da dokar ƙarin albashin.
Agbu Kefas ya bayyana hakan ne a lokacin da yake hira da manema labarai jim kaɗan bayan rattaba hannu a kudirin karin kasafin kuɗi, The Nation ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna ya rattaba hannu a karin kasafi
A rahoton Leadership, gwamnan ya sa hannu kan ƙarin kasafin kuɗin jihar Taraba na 2024 a ofishinsa da ke gidan gwamnati a Jalingo.
"Tuni shugaban ma’aikata da kwamitinsa suka dukufa wajen tsara yadda za a aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi, kuma da zaran sun dawo gare ni zan sa hannu," in ji shi.
Gwamna Kefas ya yabawa majalisar Taraba
Dangane da ƙarin kasafin kuɗin kuma, Gwamna Kefas ya fara yabawa ƴan majalisar dokoki bisa yadda suka amince da kudirin cikin ƙanƙanin lokaci.
Agbu Kefas ya ba da tabbacin cewa zai yi duk mai yiwuwa wajen ganin ya sauke nauyin da Allah ya ɗora masa na jagorantar al'ummar jihar Taraba.
Ya ce gwamnatinsa za ta yi komai a buɗe kuma za ta tunkari duk wasu matsaloli na kudi da suka taso domin cika alƙawurran da ya ɗauka kafin a zaɓe shi.
Ma'aikatan jihar Kebbi za su warwasa
A wani rahoton kuma Gwamna Nasir Idris ya yi alƙwari da zaran an kammala tsara komai, zai fara biyan ma'aikata sabon mafi karancin albashi a Kebbi.
Nasir Idris Kauran Gwandu ya ce gwamnatinsa ta shirya fara biyan sabon albashin ba kamar yadda wasu ke yaɗawa ba
Asali: Legit.ng