Kano: Kamar Sokoto, an Jefa Dan Jarida a Kurkuku kan Sukar Abba da Sanusi II

Kano: Kamar Sokoto, an Jefa Dan Jarida a Kurkuku kan Sukar Abba da Sanusi II

  • An cafke wani dan jarida a Kano tare da tasa keyarsa zuwa gidan gyaran hali kan sukar Abba Kabir Yusuf da Muhammadu Sanusi II
  • Matashin mai suna Muktar Dahiru da ke aiki da gidan rediyon Pyramid FM ya shiga hannu a jiya Alhamis 29 ga watan Agustan 2024
  • Hakan bai rasa nasaba da yada wasu hirarraki da faifan bidiyo da ake ganin cin mutuncin gwamnan ne a jihar da kuma Sarki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Wani dan jarida a jihar Kano ya gamu da matsala bayan tasa keyarsa zuwa gidan yari.

Ana zargin an cafke Muktar Dahiru ne saboda sukar Gwamna Abba Kabir da Sarki Muhammadu Sanusi II.

Kara karanta wannan

An cafke dattijo da zargin kasuwanci da yan bindiga a bidiyo, ya fadi lambar wayarsu

An kama dan jarida da yada bayanai da ke cin mutuncin Abba Kabir da Sarki Sanusi II
An cafke dan jarida kan zargin cin mutuncin Gwamna Abba Kabir da Sarki Sanusi II a Kano. Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Abba Kabir Yusuf.
Asali: Facebook

Gwamnatin Kano ta cafke dan jarida

An kama dan jaridar da ke aiki da gidan rediyon Pyramid FM tare da garkame shi a jiya Alhamis 29 ga watan Agustan 2024, cewar Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin na zargin Dahiru ya yada wasu bayanai da ake ganin sun shafi cin mutuncin gwamnan da kuma Sarki Sanusi II.

Dahiru ya wallafa murya a wata ganawa da aka yi da dan adawa da ke zargin gwamnan jihar kan cin hanci da rashawa.

Kano: Abin da ake zargin dan jarida

Har ila yau, Dahiru ya wallafa wata murya da ake sukar Sarki Sanusi II da cewa yana nuna tausayin talakawa amma kuma yana rayuwa mai tsada da kawa kamar mace.

Sannan Dahiru ya wallafa wata hira da wani dan adawa ke zargin Rabiu Kwankwaso da almundahanar N320m na kudin takara.

Kara karanta wannan

Yayin da ambaliya ke rusa gidajen Kaduna, gwamnatin Uba Sani za ta gina sabon birni

An gurfanar da Dahiru a sirrance a kotun majistare da ke kan hanyar Gyadi Gyadi kan zargin bata suna hadin baki da kuma cin mutunci.

Kotun ta umarci tsare Dahiru a gidan gyaran hali har zuwa ranar 3 ga watan Satumbar 2024 domin neman belinsa.

An kama hadimin Tambuwal a Sokoto

Kun ji cewa rundunar yan sanda a jihar Sokoto ta gurfanar da hadimin Sanata Aminu Tambuwal kan cin zarafin gwamna.

Ana zargin Shafi'u Tureta da cin mutuncin Gwamna Ahmed Aliyu inda ya wallafa faifan bidiyo da cewa bai iya yaren Turanci ba.

Tureta ya kuma yada takardar sakamakon gwamnan na sakandare da cewa yayi mummunan faduwa a wasu darusa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.