“Za Mu Saka Kafar Wando Daya da Ku”: Majalisar Tarayya Ta Ja Kunnen Al'umma

“Za Mu Saka Kafar Wando Daya da Ku”: Majalisar Tarayya Ta Ja Kunnen Al'umma

  • Majalisar Tarayya ta nuna bacin ranta kan kokarin bata sunan Majalisar da kuma mambobinta da al'umma ke yi
  • Majalisar ta gargadi 'yan Najeriya da su yi hankali saboda ba za ta zuba ido tana gani ana ci mata fuska ba a kasar
  • Wannan na zuwa ne bayan zargin shugaban masu rinjaye, Opeyemi Bamidele da neman a ba kamfaninsa kwangila

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Majalisar Tarayya ta gargadi 'yan Najeriya kan bata sunan shugabanni da mambobinta.

Majalisar ta ce ba za ta zuba ido wasu na kokarin goga mata bakin fenti da kuma shuabanninta ba.

Majalisar Tarayya ta gargadi wasu 'yan Najeriya kan kokarin bata mata suna
Majalisar Tarayya ta ja kunnen wasu 'yan Najeriya kan bata sunanta da shugabanninta. Hoto: Nigerian Senate.
Asali: Facebook

Majalisar Tarayya ta gargadi wasu 'yan Najeriya

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta yi magana kan zargin shirin korar Ganduje daga mukaminsa

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin Opeyemi Bamidele ya fitar a yau Juma'a 30 ga watan Agustan 2024, Punch ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce Majalisar ta yi Allah wadai game da zarge-zarge kan shugaban masu rinjaye, Opeyemi Bamidele.

Ta ce hakan wani kokari ne na kawo rudani da kuma rashin aminci tsakanin al'umma da Majalisar, cewar Vanguard.

"Majalisa ba ta ji dadin zarge-zarge kan Bamidele ba kuma za ta dauki mataki saboda kokari ne na neman bata sunan Majalisar da shugabanninta."

- Cewar sanarwar

Musabbabin gargadin Majalisar ga 'yan Najeriya

Wannan na zuwa ne bayan wata kungiya ta kai korafi ga hukumar ICPC da zargin Bamidele yana kokarin tilasta shugaban hukumar REA ya ba shi kwangila.

Shugaban kungiyar Public Procurement Transparency, David Udoh ya zargi Bamidele da neman shugaban REA, Abba Aliyu ya ba kamfaninsa kwangila daga kwangilolin hukumarsa.

Kara karanta wannan

Atiku da Obi sun yi martani kan inyamura mai ikirarin kashe yan Najeriya a Canada

Majalisa ta magantu kan albashin mambobinta

Kun ji cewa Majalisar Dattawa ta musanta cewa ana biyan sanatoci N21m a matsayin albashi da kuɗin alawus-alawus.

Majalisar ta musanta hakan ne a cikin wata sanarwa biyo bayan kalaman da Sanata Kawu Sumaila ya yi na cewa yana samun kusan N22m duk wata.

Kakakin Majalisar Dattawan, Sanata Adeyemi Adaramodu ya yi ƙarin haske kan lamarin ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a birnin Tarayya Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.