Atiku da Obi Sun Yi Martani kan Inyamura Mai Ikirarin Kashe Yan Najeriya a Canada

Atiku da Obi Sun Yi Martani kan Inyamura Mai Ikirarin Kashe Yan Najeriya a Canada

  • Wata inyamura da ke zaune a kasar Canada, Amaka Sunnberger ta ja hankalin manyan kasar nan saboda barazanar kashe jama'a
  • An gano Amaka Sunnberger ta wata hira da su ka yi a manhajar Tik Tok ta na barazanar kashe Yarbawa da yan Benin da guba
  • Tsofaffin yan takarar shugaban kasa a Najeriya, Atiku Abubakar da Peter Obi sun hada baki wajen tir da wannan danyen aiki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi Allah wadai da ikirarin Amaka Sunnberger na shirin kashe wasu kabilun kasar nan.

Kara karanta wannan

Likitoci sun fadi abin da ke korarsu zuwa neman aiki a kasashen waje

Matar ta yi barazana za ta kashe Yarbawa da yan kasar Benin da ke zaune a Canada ta hanyar ba su guba, kuma ta ce babu wanda ya isa ya kama ta.

Atiku
Atiku Abubakar, Obi sun yi tur da ikirarin wata inyamura na kashe 'yan Najeriya a Canada Hoto: Atiku Abubakar/@PeterObi
Asali: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku Abubakar ya ce furucin Amaka abin kyama ne kwarai da gaske.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon dan takarar shugaban kasa a shekarar 2023 ya kuma yabawa majalisar kasar nan da ta yi gaggawar mika bayanan masu kitsa kisan ga hukumomin Canada.

Obi ya fusata da ikirarin kashe 'yan Najeriya

Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter Obi ya ce abin takaici ne yadda wasu ke son ganin bayan wata kabila a Najeriya.

Mista Obi ya ce abin da ya dace a mayar da hankali a kai shi ne gina kasar nan domin ci gaba da samar da wanzuwar zaman lafiya ma dorewa.

Kara karanta wannan

Malaman addini sun samo dabara, an nemowa Tinubu hanyoyin rage tsadar abinci

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, tsohon dan takarar ya ce yanzu ba lokaci ne na rarrabuwar kai a kasar nan ba.

Cuta ta kashe 'yan Najeriya

A wani rahoton kun ji yadda aka samu bullar sabuwar cutar mashako a jihar Kano da ta yi sanadiyyar rasuwar mutane akalla 40 a asibitin zana da ake kira IDH.

Rahotanni sun tabbatar da cewa kullum sai an samu asarar rai yayin da asibitin IDH ya cika taf, ita kuma hukumar asibitocin Kano na taron gaggawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.