Harin Ƴan Bindiga Ya Fusata Gwamna, Za a Sake Buɗe Sansanin Sojoji a Arewa

Harin Ƴan Bindiga Ya Fusata Gwamna, Za a Sake Buɗe Sansanin Sojoji a Arewa

  • Gwamnatin jihar Neja ta sanar da cewa sojoji sun fara tantance yanayin tsaro a Alawa domin duba yiwuwar sake buɗe sansani
  • Muƙaddashin gwamnan jihar Neja, Yakubu Garba ne ya bayyana hakan biyo bayan harin da ƴan bindiga suka kai garin kwanan nan
  • Sanata Mohammed Sani mai wakiltar Neja ta Gabas ya ba da tallafin kayan abinci a rabawa waɗanda harin ya rutsa da su a Alawa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Niger - Mukaddashin Gwamna jihar Neja, Yakubu Garba ya sanar da cewa rundunar sojoji ta fara tantance yanayin tsaro a garin Alawa da ke jihar.

Yakubu Garba ya bayyana cewa hakan zai ba da damar sake buɗe sansanin sojoji a garin Alawa, wanda a baya-bayan nan ya fuskanci hare-haren ƴan bindiga.

Kara karanta wannan

Hankula sun kwanta da sojoji suka fadi lokacin dakile matsalar tsaro, an samu cigaba

Gwamna Muhammad Umaru Bago.
Gwamnatin Neja ta haɗa kai da sojojin domin sake buɗe sansani a garin Alawa Hoto: Muhammed Umaru Bago
Asali: Twitter

Mukaddashin gwamnan ya faɗi haka ne a gidan gwamnati dake Minna bayan ya karbi tallafin abinci daga Sanata Mohammed Sani mai wakiltar Neja ta Gabas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata ya bada tallafi a Neja

Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, Sanatan ya ba da tallafin kayan abincin ne domin a rabawa mutanen da harin ƴan bindiga ya rutsa da su a Alawa.

Yakubu ya ƙara da cewa zaman lafiya ya fara dawowa a kauyen Barkuta da ke ƙaramar hukumar Bosso biyo bayan rikicin manoma da makiyaya wanda ya jawo asarar rayuka.

Tawagar da sanatan Neja ta Gabas ya aiko karƙashin jagorancin Babasule Bisala sun miƙa tallafin kayan abincin ga muƙaddashin gwamnan.

Sun ce sun zaɓi miƙawa gwamnatin Neja tallafin ne saboda ba za su iya zuwa da kansu su rabawa mutanen da harin ƴan bindigar ya rutsa da su ba.

Kara karanta wannan

Kaduna: Ƴan bindiga akalla 8 sun baƙunci lahira da suka yi arangama da sojoji

Yadda aka kashe manoma a Niger

Harin na baya-bayan nan ya yi sanadin mutuwar manoma 13 da suka bar sansanin ‘yan gudun hijira domin zuwa gonakinsu.

Hakimin Alawa, Ibrahim Salihu ya ce an gano wadanda harin ya rutsa da su, ya kuma tabbatar da cewa tallafin zai isa gare su da kuma iyalan wadanda aka kashe a harin.

Ana sa ran sake bude sansanin soji zai kawo sauki ga mazauna yankin da kuma ba manoma damar ci gaba da harkokinsu na noma.

Niger: Jami'an tsaro sun tono bama-bamai

A wani rahoton kuma jami'an tsaro sun tono abubuwan fashewa da bama-bamai a garuruwa daban daban a wasu sassan jihar Neja.

Mai magana yawun ƴan sanda, SP Wasiu Abiodun ya ce sun gano waɗannan miyagun makamai ne tsakanin 2021 zuwa 2023.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262