Likitoci Sun Fadi Abin da Ke Korarsu zuwa Neman Aiki a Kasashen Waje

Likitoci Sun Fadi Abin da Ke Korarsu zuwa Neman Aiki a Kasashen Waje

  • Kungiyar likitoci ta kasa ta bayyana dalilin da ya sa da yawa daga cikin jami'an lafiya ke neman aiki a waje
  • Gwamnatin tarayya da sauran yan kasar nan na nuna damuwa kan yadda likitoci ke fita kasashen waje yin aiki
  • A martaninta, NMA ta bayyana cewa rashin tsaro da ya yi kamari ya sa wasu daga cikinsu neman mafaka a kasar waje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kogi - Kungiyar likitoci ta kasa (NMA) ta dora alhakin yawaitar fita yin aiki kasashen waje kan rashin tsaro a kasar nan.

Kungiyar NMA ta bayyana cewa rayuwar likitoci na cikin hadari, shi ya sa su kan gwammace su fita yin aiki kasar waje.

Kara karanta wannan

Mata sun zargi rundunar sojojin kasa, sun nemi a janye dakaru daga yankin Ibo

Likitoci
Likitoci sun fadi dalilin gudawa aiki kasar waje Hoto: Pius Utomi Ekpei
Asali: Getty Images

Channels Television ta wallafa cewa shugaban kungiyar reshen jihar Kogi, Abubakar Hassan ne ya bayyana haka a Lokoja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya na bayani ne kan yajin aikin da likitocin kasar nan su ka tsunduma saboda rashin tsaro.

Dalilin fitar likitoci kasar waje

Kungiyar likitoci ta kasa (NMA) ta bayyana cewa yanzu miyagu sun mayar da su ababen farauta, Jaridar Punch ta wallafa.

Shugaban kungiyar a Kogi, Dr. Abubakar Hassan da ya bayyana haka ya yi takaicin yadda ake samun karuwar sace jami'an lafiya a Kebbi.

Yawaitar sace likitoci a Najeriya

Kungiyar NMA ta bayyana cewa yawan sace likitoci da ake yi ya na kassara sashen kiwon lafiya a Kebbi da kasa baki daya, kuma hakan babbar barazana ce.

Shugaban NMA a jihar, Dr. Abubakar Hassan ne ya bayyana haka, ya ce 'yan ta'addan sun rufe idanunsu, ba sa la'akari da aikin ceton rai da likitoci ke yi.

Kara karanta wannan

Atiku da Obi sun yi martani kan inyamura mai ikirarin kashe yan Najeriya a Canada

Likitoci sun tafi yajin aiki

A baya mun ruwaito cewa likitoci a sun fara yajin aikin gargadi domin nuna takaicin yadda yan bindiga ke sace su, musamman a Kaduna.

Kungiyar NARD ta tsunduma yajin aikin mako guda domin karkato da hankalin gwamnati kan matsalar sace su da miyagu su ka yawaita yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.