Malaman Addini Sun Samo Dabara, An Nemowa Tinubu Hanyoyin Rage Tsadar Abinci

Malaman Addini Sun Samo Dabara, An Nemowa Tinubu Hanyoyin Rage Tsadar Abinci

  • Hauhawar farashin abinci na ci gaba da ta'azzara matsalar abinci a sassan kasar nan baki daya
  • Hakan ta sa malaman addinin kirista na darikar katolika su ka bijirowa shugaban kasa wasu dabaru
  • A taron da su ka yi a Edo, sun shawarci gwamnatin Bola Tinubu ta magance matsalar yunwa da ake ciki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Edo - Malaman addinin kirista sun shawarci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya rungumi dabarun rage tsadar farashin abinci a kasa.

Malaman sun bayyana haka ne a taron limaman darikar katolika da ya gudana a Auchi da ke jihar Edo.

Kara karanta wannan

Mata sun zargi rundunar sojojin kasa, sun nemi a janye dakaru daga yankin Ibo

Bishop
Bishof na darikar katolika sun shawarci shugaba Tinubu kan magance tsadar abinci Hoto: Bishop Shanahan Bulletins
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa a jawabin bayan taro, malaman sun tunatar da gwamnati cewa akwai yunwa sosai a kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar malaman ta kara da cewa ba zai yiwu su na kiran talakawa su yi hakuri ba, su kuma yan siyasa na rayuwarsu ba tare da tuna nauyin jama'a ba.

An jerowa Tinubu dabarun rage tsadar abinci

Bishof din katolikan sun shawarci shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba manoma bashi mai saukin ruwa da iri mai inganci domin habaka yabanya.

Jaridar The Cable ta wallafa cewa shugaban kungiyar, Lucius Iwejuru ne ya nemi haka a sakon bayan taro da ya sanyawa hannu.

Dalilin neman daukin Tinubu kan tsadar abinci

Kiristocin kasar nan sun tunatar da gwamnatin tarayya cewa talakawa na cikin kunci da yunwa da rashin abin hannu, saboda haka a taimaki masu kananan sana'o'i.

Kara karanta wannan

Likitoci sun fadi abin da ke korarsu zuwa neman aiki a kasashen waje

Kungiyar malaman na katolika ta bayyana cewa bai kamata a ce talakawa na shan wahala, amma an samarwa wasu shafaffu da mai hanyar hutu ba.

Talakawa na rage ci saboda tsadar abinci

A wani labarin kun ji cewa wasu daga cikin mazauna kasar nan sun ce hauhawar farashin kayan abinci ya sa ba sa iya cin abinci yadda su ka saba.

Wasu daga cikin mazauna Kaduna sun bullo da dabarun girki sau biyu, yin azumin kwana biyu da rage yi wa baki tayin abinci domin rage yawan cin abinci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.