Boko Haram Ta Kai Hari kan Yan Shi’a, an Harbe Mutane har Lahira

Boko Haram Ta Kai Hari kan Yan Shi’a, an Harbe Mutane har Lahira

  • Wasu yan ta'adda da ake zargin yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari kan yan kungiyar Shi'a a jihar Yobe da ke Arewacin Najeriya
  • Bayanai sun tabbatar da 'yan ta'addar sun kai hari ne makarantar Faudiyya a ƙaramar hukumar Geidam yayin da dalibai ke barci
  • Wani dan banga da ya shaida lamarin ya bayyana cewa yan ta'addar sun harbe wasu daliban makarantar har lahira yayin harin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Yobe - Wasu yan ta'adda da ake zargin yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari kan makarantar Shi'a ta Faudiyya a Yobe.

Rahotanni sun nuna cewa yan ta'addar sun kai hari ne cikin dare a lokacin da dalibai ke cikin barci.

Kara karanta wannan

Yan bindiga kimanin 30 sun dura karamar hukuma, sun cinna wuta da harbe harbe

jihar Yobe
An kai hari kan yan Shi'a a Yobe. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa an samu hasarar rayuka a yayin da yan ta'addar suka kai hari makarantar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Boko Haram ta kai hari wajen yan Shi'a

Wasu yan bindiga da ake zargin yan Boko Haram ne sun kai hari kan makarantar Faudiyya ta ƙungiyar Shi'a.

Rahoto ya nuna cewa lamarin ya faru ne a makarantar Faudiyya da ke karamar hukumar Geidam kuma an samu harasar rayuka.

Boko Haram ta kashe yan Shi'a 3

Wani dan banga ya bayyana cewa yan ta'addar sun fito da yan makarantar Shi'a guda uku da misalin karfe 3:44 na safiya suka bude musu wuta har lahira.

Haka zalika ya tabbatar da cewa wani dalibi da yaso guduwa ya samu raunuka kuma yana kwace a gadon asibiti.

Bayanin jami'an tsaron jihar Yobe

Aminiya ta wallafa cewa kakakin yan sanda a jihar Yobe, SP Dungus Abdulkarim ya tabbatar da faruwar lamarin sai dai bai yi karin haske ba.

Kara karanta wannan

Fargaba a Abuja: 'Yan bindiga sun harbe magidanci, sun sace matarsa da yaransu

Mataimakin daraktan yada labaran rundunar Operation Lafiya Dole, Kyaftin Shehu Muhammad ya ce zai tuntubi manema labarai da zarar sun samu karin haske kan lamarin.

Yan sanda sun zargi yan Shi'a da laifi

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban yan sanda, Kayode Egbetokun ya ba jami'ansa zazzafan umarni kan yan kungiyar Shi'a bayan sun yi arangama a Abuja

Rundunar yan sanda ta zargi yan kungiyar Shi'a da kai musu farmaki a yayin da suka fito tattaki a ranar Lahadi a birnin tarayya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng