Yara 'Yan Kasa da Shekara 18 Sun Tafi Kurkuku kan 'Yunkurin' Kifar da Gwamnati
- Babbar kotu da ke zamanta a Abuja ta aika da wasu mazauna kasar nan da aka kama lokacin zanga-zanga zuwa kurkuku
- An kama su ne bisa zargin ta'addanci da neman kifar da gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu lokacin da aka fito tituna
- Jama'ar kasar nan sun yi zanga-zangar adawa da yunwa da manufofin shugaba Tinubu da ake zargi sun jawo matsaloli
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Babbar kotun tarayya da ke zamanta ta Abuja ta aika mutane 75 da ake zargi da yin zanga-zangar adawa da gwamnati zuwa kurkuku.
Yan sanda sun cafke wasu daga wadanda ake zargi da tayar da hatsaniya a lokacin zanga-zanga da aka gudanar a kasar nan ta tsawon kwanaki 10.
Jaridar Premium Times ta wallafa cewa 28 daga cikin mutanen da aka aika kurkukun yara ne da shekarunsu suka gaza 18.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tsare masu zanga-zanga a kurkuku
Rundunar yan sanda ta nemi a tsare wadanda aka kama lokacin zanga-zanga na tsawon watanni biyu domin ba su damar bincike.
Sufeto Janar na yan sanda, Kayode Egbetokun na zargin mutanen da ta'addanci, rike makami da bisa ka'ida ba da cin amanar kasa.
An yi tir da tsare yara a kurkuku
A sakon da ta wallafa a shafin X, kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty Int'l ta caccaki gwamnati kan tsare yara yan kasa da shekara 18.
Kungiyar ta nemi hukumomin kasar nan su gaggauta sakin yaran domin su koma gaban iyayensu.
Za a bibiyi yaran da ke kurkuku
Kwamitin zaman lafiya na jihar Kano ya bayyana cewa fargabar wannan matsalar na daga cikin dalilansu na rokon iyaye su killace yaransu lokacin zanga-zanga.
Shugaban kwamitin, Ambasada Ibrahim Waiya ya shaidawa Legit cewa za su nemi sauran kungiyoyi domin ganin yadda za a kubuto da yaran zuwa gudajensu.
Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga
A lokacin kun ji cewa rundunar yan sanda ta fatattaki masu zanga-zanga da suka taru a kofar fadar Mai Martaba Sarkin Bauchi don ganawa da sarkin.
Jami'an tsaron sun baza borkonon tsohuwa yayin da jama'a ke kokarin nuna adawa da manufofin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da tsadar rayuwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng