An Harbe Ƙasurgumin Ɗan Bindiga da Ya Sace Manyan Mutane a Najeriya
- Rundunar yan sandan Akwa Ibom ta sanar da cafke wani ƙasurgumin shugaban yan bindiga mai garkuwa da mutane
- Rahotanni sun nuna cewa yan sanda sun harbe babban dan bindigar ne bayan sun yi musayar wuta a wani fada da suka yi
- Dan bindigar ya shahara da sace manyan ma'aikatan gwamnati da yan kasuwa bayan talakawa da yake garkuwa da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Akwa Ibom - Rundunar yan sanda ta fafata da wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ake nema ido rufe.
An ruwaito cewa yan sandan Najeriya sun yi nasarar hallaka dan bindigar bayan sun yi musayar wuta.
Jaridar Punch ta wallafa cewa yan sanda sun kwato makaman da dan bindigar ke amfani da su wajen kai hare hare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kashe babban ɗan bindiga, Condiment
Kakakin yan sanda a jihar Akwa Ibom, ASP Timfon John ya tabbatar da cewa sun kashe wani babban mai garkuwa da mutane da aka fi sani da Condiment.
Lamarin ya faru ne bayan yan sanda sun yi musayar wuta da dan bindigar a yankin Uyanga da ke jihar Cross River.
Manyan mutanen da 'dan bindigar ya kama
An ruwaito cewa Condiment ya taba garkuwa da babbar alkalin kotun tarayya kuma ya kashe dan sandan da ke ba ta tsaro.
Haka zalika an zarge shi da garkuwa da kisan shugaban kamfanin Emem and Sons da kama shugaban Mingles Hotels.
An kwato makamai wajen 'dan bindigan
Daily Trust ta ruwaito cewa rundunar yan sanda ta kwato bindiga kirar G3 da tarin harsashi bayan kashe dan bindigar.
Bayanai sun nuna cewa yan sanda na cigaba da bincike kan yadda za a gano sauran yan kungiyar ta'addanci da Condiment ke jagoranta.
Yan bindiga sun kai hari a Anambra
A baya kun ji cewa rahotanni da suka fito daga jihar Anambra na nuni da cewa yan bindiga sun mamaye wani kauye kuma suka harbi shugaban tsaron garin.
Mummunan lamarin ya faru ne a yankin Obosi a karamar hukumar Idemili ta Arewa a jihar Anambra kamar yadda bayanai suka tabbatar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng