Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga Sama da 1,000, Sun Ceto Ɗaruruwan Mutane a Najeriya

Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga Sama da 1,000, Sun Ceto Ɗaruruwan Mutane a Najeriya

  • Sojojin Najeriya sun kashe ƴan ta'adda 1,166 tare da kama wasu 1,096 a watan Agusta, 2024 a sassa daban-daban na ƙasar nan
  • Mai magana da yawun hedkwatar tsaro DHQ, Edward Buba ne ya sanar da haka, ya ce sojoji sun kashe hatsabiban ƴan bindiga a Arewa
  • Ya bayyana cewa dakarun sun kuma ceto ɗaruruwan mutane da aka yi garkuwa da su, sannan sun kwato makamai a hannun ƴan ta'adda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - A ci gaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya, rundunar sojojin Najeriya ta yi nasarar hallaka ƴan ta'adda 1,166 a sassa daban-daban na kasar nan.

Dakarun rundunar sojin sun kama miyagu 1,096 tare da kubutar da mutane 721 daga hannun masu garkuwa da mutane a kwanaki 30.

Kara karanta wannan

Hankula sun kwanta da sojoji suka fadi lokacin dakile matsalar tsaro, an samu cigaba

Edward Buba.
Hedkwstar tsaro ta ce sojoji sun hallaka ƴan ta'adda sama da 1,000 a watan Agusta Hoto: DefenceinfoNG
Asali: UGC

Daraktan yada labarai na hedkwatar tsaron ta kasa (DHQ) Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manjo Janar Buba ya ce dakarun sojojin sun samu waɗannan nasarori kan ƴan ta'adda ne a cikin watan Agusta, 2024.

DHQ: Sojoji sun halaka manyan ƴan ta'adda

Da yake jawabi kan nasarorin sojoji a watan da yake mana bankwana, Buba ya ce kwamandojin ƴan ta'adda da shugabannin ƴan bindiga da dama sun baƙunci lahira.

Kakakin DHQ ya ambaci sunayen wasu manyan shugabannin ƴan ta'adda da sojoji suka tura lahira a Agusta a shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya.

Ƙasurguman ƴan ta'addan da aka kashe sun haɗa da Munir Arika da Sani Dilla (Dan Hausawan Jibilarram), Ameer Modu, Dan Fulani Fari Fari, Bakoura Araina Chikin, Dungusu, Abu Darda da Abu Rijab.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda masu yawa sun sheka barzahu bayan sojoji sun yi musu ruwan wuta

An kashe hatsabiban ƴan bindiga a Arewa

Edward Buba ya ce dakarun sun hallaka manyan ƴan bindiga a Arewa maso Yamma, daga cikinsu akwai Kachalla Dan Ali Garin Fadama da Kachalla Dan Mani Na Inna.

Sauran sun haɗa da Kachalla Basiru Zakariyya, Sani Bakatsine, Inusa Zangon Kuzi, Ibrahim, Tukur da Kamilu Buzaru.

"Har ila yau sojojin sun kwato makamai 391, alburusai 15,234 tare da hana satar mai na sama da N5bn," in ji Buba.

Ya kuma ƙara da cewa waɗannan nasarori ne dalilan da suka sa ƴan Boko Haram da ISWAP suke fitowa a kowace rana suna miƙa wuya, Leadership ta rahoto.

Sojoji sun yi nasara a Birnin Gwari

A wani rahoton kuma gwarazan sojojin Najeriya sun hallaka ƴan bindigar daji takwas a yankin ƙaramar hukumar Birnin Gwari a Kaduna.

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce sojojin sun sheƙe ƴan ta'addar ne a lokacin da suka fita sintiri a kewayen Kamfanin Doka da Gayam.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262