Sarkin Ilorin Ya Nada Gwamnan Kwara Sarautar ‘Sardauna’, Ya Fadi Tasirinta a Wajensa

Sarkin Ilorin Ya Nada Gwamnan Kwara Sarautar ‘Sardauna’, Ya Fadi Tasirinta a Wajensa

  • Gwamna AbdulRahman AbdulRasaq na jihar Kwara ya samu sarautar Sardaunan Ilorin bayan kaiwa Sarkin Ilorin ziyarar ban-girma
  • Mai martaba Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari ya ce ya ba gwamnan wannan sarauta ne saboda martabawarsa ga masarautar
  • Gwamna AbdulRahman ya nuna matukar jin dadinsa da samun wannan sarauta wadda ya ce ba irin sarautar nan ta je ka na yi ka ba ce

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ilorin, Kwara - Mai martaba Sarkin Ilorin, Dakta Ibrahim Sulu-Gambari ya nada gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRasaq sarautar Sardaunan Ilorin.

Mai martaba Sulu-Gambari ya ce ya nada gwamna wannan sarautar ne saboda ya nuna godiya ga kokarinsa na martabawa da kuma bunkasa al’adu da masarautar Ilorin.

Kara karanta wannan

Kwanaki 4 da mutuwar basarake mai daraja ta 1, masu neman sarauta 5 za su fafata

Sarkin Ilorin ya yiwa gwamnan Kwara nadin sarauta
An nada gwamnan Kwara sarautar Sardaunan Ilorin. Hoto: @RealAARahman
Asali: Twitter

Sarkin Ilorin ya jinjinawa gwamnan Kwara

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa nadin ya sanya Gwamna AbdulRahman ya zama Sardauna na biyu a masarautar Ilorin bayan mutuwar Alhaji Umar Saro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani dan takaitaccen taron bayyana sarautar, sarkin ya yabawa Gwamna AbdulRahman bisa kyakkyawan jagorancinsa da kuma kokarinsa na bunkasa muradun al’umma.

Sarkin Ilorin ya kuma yabawa gwamnan bisa rawar da ya ke takawa a jiha da kasa a matsayinsa na shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya.

Gwamna ya ji dadin sarautar sardaunan Ilorin

Gwamna AbdulRahman AbdulRasaq ya bayyana irin jin dadin da ya ji da wannan nadin sarautar da aka yi masa, inda ya yi dogon bayani a shafinsa na X.

Gwamnan ya ce:

"A yau ne na jagoranci mukarrabaina zuwa fadar mai martaba Sarkin Ilorin, Dakta Ibrahim Sulu-Gambari domin mika godiyarmu ga masarautar bisa zaman lafiya da muka samu."

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano ya yiwa fitaccen mawakin siyasa kyautar sabuwar mota, ya saki bidiyo

"A yayin ziyarar, mai martaba sarkin ya ba ni sarauta mai daraja ta Sardaunan Ilorin."
"Wannan sarautar ta na da tasiri, kuma ba sarautar je ka na yi ka ba ce. Idan muka duba tahiri, manyan mutane ne suka rike sarautar, musamman ma Sir Ahmadu Bello (CBE)."

Tinubu ya taya gwamna AbdulRahman murna

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq murnar zama shugaban kungiyar gwanonin Najeriya.

Shugaban kasar ya kuma bukaci sabon shugaban kungiyar NGF da ya yi amfani da wannan dama wajen inganta zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban kasar baki daya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.